Uba ya auri jikarsa
Wani attajiri daya auri jikarsa a bisa rashin sani yaki yarda a raba auren duk da cewa daga baya ya gane cewa amaryar tasa jikanyarsa ce.
Attajirin mai shekaru 68 ya hadu da yarinyar ne ta shafin yanar gizo, kuma ya nemi aurenta ne a jajibarin sabuwar shekara bayan sun kwashe dan kankanin lokaci suna soyayya. Shi dai Attajirin ya samu arzikinsa ne a wasan caca, kuma bai Ankara cewa amryarsa jikanyarsa bace har sai watanni uku da yin bikinsu.
Attajirin dai yana da yaya a auren da yayi a baya, sai dai yace daya daga cikin matan nasa ta tafi da yaransu, kuma bai kara ganinta ba duk da irin kokarin da yayi na nemanta. Daga nan sai ya kara auren mata ta biyu wadda ita ma suka rabu daga baya. Ganin yadda yake fama da matsalar aure ne, sai Attajirin ya fara neman yan mata ta shafin yanar gizo, inda a nan ne ya hadu kuma ya auri wata yarinya yar shekaru 24 , wadda ashe jikarsa ce.
KU KARANTA: 'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda 3
Sai bayan watannin uku da bikinsu ne ma’auratan suka gane dangantakarsu ta hanyar hotunan danginsu, inda ya ga daya daga cikin yayansa daya gudu ne mahaifin amaryarsa. Sai dai Angon yace ba shi da niyyar sakin amaryartasa, saboda yana jin dadin zama da ita, sakamakon bai ji dadin auren da yayi a baya ba.
Attajirin ango, kuma mijin jikanyarsa yace: “Abin tamkar siddabaru, amma da fari na kasa gane dalilin daya sa muka shaku da juna. Nayi aure biyu a baya, kuma bani da nufin yin na uku.”
Ita kuma zmaryar tace: “Lokacin dana ga hoton babana. Sai naji ba dadi. Shakuwar mu ta kai matuka, muna son junanmu, ban ga abinda zai raba auren mu ba.”
Abin ban mamaki da yawa yake.
Asali: Legit.ng