Liverpool zasu sayi dan wasan gaba

Liverpool zasu sayi dan wasan gaba

- Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool suna matse da sayen dan wasan gaba na Athletico Bilbao          

- Jurgen Klopp yana da tarin zaratan yan wasan gaba Sturridge, Origi, Firmino, Ings

Duk da kasan cewar Daniel Sturridge da Firmino, da Divorce Origi da Ings, amma har yanzu mai horarwar na kungiyar Jurgen Klopp yana kokarin kara sayen dan wasan gaba.

Dan gane da rohoton da muka samu daga Don Balon, kungiyar Liverpool tana son ta saye dan wasan gaba na Athlentico Bilbao Inaki Williams.

Liverpool zasu sayi dan wasan gaba
Inaki Williams

Dan shekara 22 yana taka leda da kyau, kuma yana kayatarwa, inda ya janyo hankalin kungiyoyi da dama wanda ya hada da kungiyar Liverpool da abokan hamayyar su wato Everton.

Williams,  wanda ya samu damar samun cikkaken lokacin doka wasa a spain a farkon shekarar nan, inda ya samu damar zura kwallo 8 a wasar laliga ta bara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel