Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da sassan jikin mutum

Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da sassan jikin mutum

- An damke Wole Oke da abokin sa Wasiu Adesina a Ijebu Idi-aro a Abeokuta                                                            

- An cafke mutum 2 din da sassan jikin mutum a hannun su                                      

- Ana cigaba da bin ciken wadanda ake zargin

An kama wani mutum dan shekara 38 mai suna Wole Oke da abokin sa dan shekara 30 mai suna Wasi'u Adesina, saboda laifin kisa da yin kudin tsafi.

Ofishin yan sanda na jahar Ogun sunce sun cafke Wole da abokin sa saboda an kama su da sassan mutum.

Yan sanda sun kama wasu mutane 2 da sassan jikin mutum

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kama mutanen a Ijebu, Idi-aro a garin Abeokuta, lokacin da yan sanda yakin Oke Itoku , karkashin jagoran cin DPO, CSP Abeni Ferinre suke sintiri.

Kakakin yan sanda na jahar Abimbola Oyeyeni, a cewar sa, yace wanda wadanda ake zargin sun ranta ana kare da bagar jakar leda a hannun su da suka ga yan sanda, su kuma yan sandan suka bisu suka kama su.

Yace wanda lokacin da ya duba jakar, sun ga kasusuwan mutum a cikin jakar, lokacin da ake kan binciken , Wole Oke ya tabbatar da cewa kasusuwan na yar uwar shine da ta mutu shekara 4 da suke gabata.

Ya kara da cewa wanda wani boka yace yace suka wo za'ayi masu kudin tsafi da su.

Kwamishinan yan sanda na jahar Ogun ya umurci a mika bin ciken zuwa sashen binciken manya-manyan laifuka dan cigaba da bincike.

Kuma ya bada umurnin kamo bokan da gaggawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel