Wata mata ta watsama yar aikin ta mai shekaru 10 da haihuwa

Wata mata ta watsama yar aikin ta mai shekaru 10 da haihuwa

Wata yarinya mai shekaru 10 da haihuwa, tana cikin mawuyacin hali a hannun mai gidanta.

Matar da ake cemata 'Madam Gold' an bayyana cewar ta jikkata yar aikinta mai shekaru 10 da haihuwa wanda ba'a fadi dalilin dayasa tayi mata haka ba.

Acewar mai amfani da shafin Facebook din mai suna Akwango Precious NG Agu, matar akoda yaushe tana nuna rashin godiyar ta dangane da duk wani abu da mai aikin takeyi, inda ta watsa mata ruwan zafi kuma ta sanya mata dutsen guga mai zafin gaske a jikinta.

Madam Gold da Yar aikin nata

"Abin mamaki baya karewa" wannan kyakkyawar macen, mai haske wacce ake ce mata Madam Gold dake kasuwar BBA ta Traidefair dake Legas... kayi tunanin yadda tayi amfani da dutsen guga mai zafi ta goga a jikin wannan yar yarinyar mai shekaru 10 da haihuwa, a maimakon tayi amfani da dutsen wajen goge kayan sawa.

Kuma wannan talakar karamar yarinyar tana mata aikin gida sannan kuma tana tsare mata shago duk alokaci daya.

Kuma duk da haka bai isheta ba, saida ta dora ruwan a wuta da yayi zafi saita watsa mata a jikinta, wan irin duniya muke cikine yanzu, gata kyakkyawa, kuma tanada dattako a ido, amman duk kyawon nata na banza ne tunda zuciyarta baida kyau.

Saidai ban zarge kiba, amman na zargi talauci. Domin kuwa shine kadai zai sanya mahaifiyar yarinyar nan ta barta ta tafi wani waje waida sunan yar aiki. Saboda na tabbata bazatayima yar data haifa da kanta haka ba.

Idan da ace ni gwamnatin tarayyana ne, to babu shakka gidan yari zan kaiki ki zauna acan har karshen rayuwarki, kuma a dunga baki aikin wahala kullin kinayi a can.

Kuma baki isa ki zabi abincin da kikeso ba, kullun wake za'a dunga baki wanda bai dafu ba, sannan kuma a hanaki ruwan sha. "Madam Gold, Allah ya shirye ki, mtchw"

Allah ya kyauta, me kuke gani?

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng