Wani direban BRT ya taimaki wata mata ta haifi yarinyar ta

Wani direban BRT ya taimaki wata mata ta haifi yarinyar ta

Yin abin alkairi ga mutane da bazasu taba mantawa da kaiba, to bawai yana nufin ka baiwa mutum kyautar kudi bane kadai, a'a akwai abubuwan da zakayima mutane wanda yafi karfin ka basu kyautar kudi, kuma ya sanya mutum bazai taba mantawa da kaiba.

A kwanakin baya a jahar Legas, wani direban BRT wanda ake cema Agape Enyare, aka bayyana cewar ya taimaki wata mai ciki ta haifi jaririyar ta mace.

Wani direban BRT ya taimaki wata mata ta haifi yarinyar ta
Wani direban BRT ya taimaki wata mata ta haifi yarinyar ta

Agape Enyare da jaririyar

Matar mai ciki dai an bayyana cewar tana neman mota zataje mile 2, a daidai lokacin sai nakuda ya kamata, a inda nan da nan direban ya durkusa ya taimaka mata ta haifi yarinyar nata, inda taji dadi sosai.

An kuma bayyana cewar mamar direban tana aikin amsar haihuwa ne, saboda haka haihuwa bawai wani abune mai tada hankali a wajan saba.

Na tabbata wannan matar kullun saita godema direban nan!

Asali: Legit.ng

Online view pixel