Tsokacin Kazaure game da dakatar da Abdulmumin Jibrin

Tsokacin Kazaure game da dakatar da Abdulmumin Jibrin

Dakatar da tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na Majalisar Wakilai Abdulmumin Jibrin tsawon kwaman kwana 180 na Majalisa, ya jawo masu ganin hakan dai dai ne, da wadanda suke ganin da Majalisar ta jira hukuncin kotu bisa karar da dan Majalisar ya shigar. 

Dan Majalisar Wakilai Gudaji Kazaure, ya nuna rashin goyon bayan lamarin inda yace, “A dakatar da Abdulmumin bamu goyi ba yaba, saboda bamason abin da zai tayar da futuna da zata tayarwa da mutane hankali a cikin gida, dakatar da shi bashi bane magani ba, domin sanda aka dakatar da shi sannan zai fara rigima.”

Majalisar dai ta dakatar Jibrin bayan da kwamitin ladabtarwa ya gabatar da rahotan nuna Jibrin yaki bayyana gaban kwamitin don amsa zargin zubarwa Majalisar mutunci kan zargin aringizo ko cushe a kasafin kudi.

Sai dai tsohon ‘dan Majalisar Wakilai Ibrahim Bello, yace Jibrin din ne ya jawo kansa wannan hukunci, inda yace shine ya kamata ya bayyana gaban kwamitin ya sanar da su abin da ya faru tare da hujjojinsa domin abi ba’asi, hakan zai sa ya karawa kansa daraja kuma ya nuna cewa yasan abin da yake.

Shima dai Mohammed Hamis Rimi cewa yayi "Idan yanada gaskiya Me yasa yaki halattar kwamitin da majalisar ta kafa masa Dan ya kare kansa? Me yasa kuma duk sai bayan da aka cire shi daga kwamitin da yake jagoranta sannan zaifara abinda yakira Fallasa? Majalisar Tarayya kinyi dai dai da wannan hukunci saboda babu wani Mutum da yake a saman Dokar kasa".

Haka ma dai Usman Ahmed Nuru wanda karyan banza lokacin da akeci dashi meyasa bai fasa kwaiba saeda suka cire shi daga matsayin shugaban kwamitin akan kasafin kudin da kokarin kansa yakeyi shima ba damuwan talakaba sunyi daedae dasuka cireshi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel