Dan takaran APGA yace anyi magudi a zaben jihar Edo

Dan takaran APGA yace anyi magudi a zaben jihar Edo

Osaro Onaiwu yayi zargin magudi a zaben jihar Edo, da kuma dan takaran APGA yace ayi sabon lale, inda yace ba’ayi wani zaben hakika ba.

Dan takaran APGA yace anyi magudi a zaben jihar Edo
INEC

Dan takaraan gwamnan jihar Edo karkashin jam’iyyar APGA , Osaro Onaiwu,yayi kira da cewa ayi watsi da zaben da ake gudanar wa a jihar a yanzu.

Osaro Onaiwu yace: “Mutane sun fito kwansu da kwarkwatansu saboda suna son canji” kuma an mamaye zaben da cin hanci da rikici. PDP da APC sun hana mutane zabe. Wannan bas hi bane demokradiyyan da muka nema ba,wannan ba irin demokradiyyan da muke so ma yayanmu bane.

“Na nemi ayi watsi da zaben tun karfe 2 na rana saboda wannan zabe bogi ne. a inda nayi zabe, yan daban APC sun kwace akwatin zabe.

KU KARANTA: Zaben jihar Edo: Ku duba sakamakon zabe daga hukuma

A bangare guda, Gwamna Nasir El-Rufai ya musanta zargin da dan takaran jam’iyyar PDP yake masa jawabin da ya bayar ta mai magana da yawunsa Samuel Aruwan yace:

“Malam Nasir El-Rufai bai je jihar Edo ba a jiya, Laraba 28 ga watan Satumba sabanin tatsuniyar da daya daga cikin yan takaran yayi a gidan Talabijin.

Kana gwamna Adams Oshiomhole ya karyata maganan cewa gwamna Nasir El-Rufai ya je Jihar. Ya yi bayani ne saboda kawai a tabbatar da cewa karya ake yi, Duk da cewa doka bata hana kowani dan kasa ya je ko ina a cikin kasan ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng