Hanyoyi 6 da Arewa ta tabbatar da karfin mulkinta a Najeriya
Yankin Arewacin Najeriya yanki ne daya kunshi yawancin Hausawa da Fulanin kasar Najeriya, sa’annan yankin ya kunshi kaso mafi girma na al’ummar musulman kasar, duk da cewa akwai sauran kabilu da dama, da addinai daban daban, amma hakan bai hana yankin nuna karfin ikonta ba a Najeriya ta hanyar mamaye mulkin kasar tun kafin kafa kasar Najeriya.
Ga wasu hanyoyi guda shida da al’ummar Hausa Fulanin yankin Arewa suka mamaye mulkin Najeriya kamar yadda shaharariyar marubuciya Leena Koni Hoffmann ta rubuta a wani makalar ta.
1. Zuwan Danfodio
Sai da Musulunci yayi karfi a yankin Arewa da shekaru aruaru kafin ya watsu sauran kudancin Najeriya sakamakon jihadin da Shehi Usman Danfodio yayi a kasar Hausa daga shekarar 1754-1817.
Danfodio shi ne babban malami daya fito daga kabilar Fulani wanda ya tabbatar da muslunci a kasar Hausa sa’annan ya gina daular musulunci a Sokoto inda hakan ya sanya al’ummar Huasa Fulani suka zamto mutane masu ilimi kuma wayayyu, da haka daular Danfodio ta zamto daula mafi girma a nahiyar Afirka. Daular Danfodi ta kunshi duk masarautun kasar Hausa.
Daular Danfodio ta kwashe shekaru 100 tana mulkin yankin Sudan, tsawon lokacin da ta kwashe ya sanya kulla alaka tsakanin sarakunan Fulani da jigajigan attajiran Huasawa daga nan ne aka fara shuka karfin ikon Hausa Fulani akan sauran makwabtan yankunan. Wannan karfin mulkin ya cigaba har bayan karya daular Danfodi da turawa suka yi, asali ma turawa sun kara ma Hausa Fulani karfin iko ne saboda tsarin mulki a kaikaice da suka zo da shi inda suke amfani da sarakuna wajen mulkar al’ummominsu.
2. Zuwan Turawan mulkin mallaka
A shekara 1903 ne turawa suka karya daular Danfodi suka kwace mulki, sa’annan suka kakaba ma al’ummar Arewa mulkin mallaka. Sai dai hakan ya kawo tsarin mulki mai inganci fiye da wadda suka tarar sarakunan karshen zamanin daular Danfodio ke gudanarwa. Amma sakamakon sun tarar da jama’ar Arewa a waye, sai suka yi amfani da tsarin mulki na kaikaice, wanda hakan ya kara ma sarakuna karfi, inda su kuma turawan suke juya sarakunan.
3. Yawan al’umma
Kasar Arewa nada al’umma da yawansu ya kai kasha 60 na jimillar yawan jama’ar Najeriya, bincike ya nuna akwai mutane miliyan 92 a Arewa, sa’annan ga fadin kasa da yakai kasha biyu bias ukun jimillar fadin kasar Najeriya.
KU KARANTA: Al'amurorin da suka durkusar da yankin Arewa
Duk da kirkiran sabbin jihohi da akayi a shekarar 1967 inda janar Aguyi Ironsi shugaban mulkin soja ya kirkiri jihohi 19, amma hakan bai hana Arewa rawar gaban hantsi ba, sai dai ya samar ma kananan kabilu yanci daga hannun Hausa Fulani. Kabilun da suka fi girma a Arewa sune Hausa, Fulani da Kanuri, kuma yawancin su musulmai ne, duk da cewa akwai mabiya addinin kirista dake zaune a jihohin nan, amma dai za’a iya cewa addinin daya fi karfi a Arewa shine musulunci.
4. Samun yancin kai
Tun bayan samun yancin Najeriya daga kasar Birtaniya a 1960, kusan dukkanin mulkin kasar na hannun yan Arewa ne. sai dai kasancewar yan Arewa ke juya akalar mulkin Najeriya bayan samun yanci, hakan bai yi ma al’ummar kudancin kasar dadi ba, wanda ya zamto batun cecekuce tsakanin yankunan biyu, wannan rigimar ce ta fara shimfida fara tunanin komawa da mulkin dimukradiya, amma hakan bai yiwu ba sai a shekarar 1998.
A wannan lokaci ne aka sanya tubalin bunkasar karfin mulkin Arewa a Najeriya yayin da Alhaji Ahmadu Sardauna, jikan Shehu Usmanu Dan Fodio da sauran ya jagoranci kafa jam’iyar mutane Arewa (NPC) tare da sauran jigajigan sarakuna da yan bokon Arewa, NPC ta zamto jam’iya daya tilo data mamaye dukkanin garuruwa Arewa, hakan ya sanya ta zamto jigo a gwamnatin kasar baya dag a mulkin yankin Arewa.
Sardauna yayi amfani da NPC wajen tabbatar da adalci tsakanin HausaFulani da sauran kananan kabilun Arewa, ya samar da ababen more rayuwa da dama ga mutanen Arewa. Har zuwa yanzu, al’ummar Arewa na ganin Sardauna shi ne shugaba mafi adalci da sanin ya kamata daya taba fitowa daga Arewa. Tubalin da Sardauna ya gina shi ne ya samar da shugabancin da yan Arewa suka dinga yi a Najeriya a bayansa, shuwagabannin sun hada da Tafawa balewa, Yakubu Gowon, Murtala Muhammed, Shehu Shagari, Muhammadu Buhari, Ibrahim Babangida, Sani Abacha, da Umaru Yar’adu.
Adalcin da Sardauna ya nuna ma kananan kabilun Arewa tare da cudanya da harshe Hausa da yagi karfi a yankin, hakan sai ya sanya yaren Hausa kasancewa yare mafi karfi da sukin sadarwa tsakanin jama’an yankin, wannan ya kara hada kan mutanen Arewa.
5. Mulkin soja
Har a cikin Sojoji, yan Arewa sune suke da karfi sakamakon yawan manyan jami’anta, sanadiyyar haka yan siyasa, sarakuna, yan book da attajiran Arewa sun samu alfarma sosai da sosai daga dukkanin gwamnatocin mulkin soja da aka yi a Najeriya. An samu shuwagabannin soja yan Arewa guda shida, wanda suka hada da Yakubu Gowon, Murtala Muhammed, Shehu Shagari, Muhammadu Buhari, Ibrahim Babangida da Sani Abacha,
Kishi tsakanin Arewa da kudancin kasar nan ya munana ne bayan shugaban kasa na mulkin soja kuma dan yankin Arewa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ya soke zabukan daya gudana a zamaninsa inda wani attajirin kuma musulmi daga kabilar yarbawa na kudancin Najeriya Moshood Abiola ya lashe zaben bayan ya kada Bahsir Tofa, bahaushe dan Arewa, daga nan ne fa takun saka ya karu tsakanin Arewa da Kudu. Bayan shudewar gwamnatin Babangida, sai janar Sani Abacha ya hau karagar mulki inda shima ake ganin ya cigaba da nuna bambamci ga al’ummar kudancin kasar nan, kai har ma ta kai gay a daure Moshood Abiola a gidan yari, inda ya rasu a can.
6. Dawowar mulkin Damokradiyya
Najeriya ta dawo tsarin mulkin farar hula bayan rasuwar janar Sani Abacha, inda shuagabn kasa Abdulsalam Abubakar ya shirya zabukan fararen hula kuma ya sauka daga mulki.
Sakamakon rigingimu da suka cigaba da faruwa a Najeriya sakamakon rashin adalci da ya Kudanci suke zargin Arewa na musu, hakan ya sanya manyan Arewa suka gamsu da koke tare da korafi da al’ummar kudu suke yi, sai su manyan Arewan suka shirya tsarin mulkin karba karba a wani yarjejeniya na gemu da gemu.
A cikin yarjejeniyar an yarda babu wani dan Arewa da zai tsaya takarar zaben shugaban kasa a 1999, wannan yarjejeniya da yan Arewa suka jagoranta ya kara musu kima da kwarjini a idanun saurana yankunan kasar nan. sanadiyyar haka da dama daga cikin yan Arewa suka samu rike matsayi iri iri a gwamnatin da aka kafa duk da cewa dan kudu ne ke jagorantar ta.
Daga karshe, duk yan Najeriya sun tabbtar da cewa zaman lafiya da cigaba, tare da magance matsalolin da Arewa take fuskanta nada alaka da kawo dawwamammen zaman lafiya a kasa baki daya.
Asali: Legit.ng