Wata mata taje zubda ciki ammaa canza shawara
Rainon da yana da yana da wahala, amma wahalar tafi yawa in kayi rainon kai kadai, shiyasa yan mata da yawa suna jin tsoron samun ciki.
Amma wannan matar ta shirya ta fuskanci komai dan dana dadin uwa. Mutane suna tuna ranakun haihuwar su, da na aure, ko kammala wani abu da sauran su, amma ta banagaren soyayya ce bazan manta ba..
Yarinyar tace" zan iya tuna duk abunda ya faru shekara 2 da ta wuce, ta tafi dakin shan magani dan zubar da ciki, da tunanin zubar da cikin shine hanya mafita, sai dai niyyar ta bata cika ba.
Tana dakin shan magani ita kadai tana kuka, daga baya sai tayi rubutu kamar haka" Yau ina da muradin zubda ciki, na gama yanke shawara, saurayina yana cin amanata, samun haihuwa da shi ze zama abun kunya, na cigaba da fada ma kaina.
Banda kowa kuma banda zabi, ina zaune bana ganin kowa saboda hawaye na da ke zuba, inajin mutanen kusa dani suna fira, ni kuma na karaya.
Malamar asibiti ta kirani lokacin da za'a man aiki, sai na dauko jakar hannuna da dauko katin shaida sai naga katin da wasu ma'aurata suka bar man kwana2 da suka wuce..
A jikin katin akwai ayar bible"kada kiji ko kaji tsoro, ina tare da ku, karka raunana, saboda ni ubangijin ku ne, zan karfafa maku kuma in taimake ku, zan daukaka ku da hannu na mai rahama.
Kawai sai na fito waje da gudu na fashe da kuka, sai kuma naji raina yayi sanyi.
Yanzu ina ganin nice uwa mafi farin ciki a duniya.
Asali: Legit.ng