Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

- Abin takaici ne yadda sauran yankunan kasar nan suke alakanta yankin Arewa da ta’addanci

- Jama’a da dama suna tunanin gaba ta’addanci ya mamaye gaba daya yankin Arewa, don haka ba wurin zuwa bane

- A gaskiya wannan ba daidai bane, domin kuwa akwai wurare da dama da mutum zai iya kai ziyara don shakatawa da yawon bude ido, Ba kamar yadda ake tunani ba, ba’a harbe harbe a irin wuraren nan

Daya daga ciki ireiren wuraren shi ne dajin Yankari, dajin yankari wuri ne da zai kayatar da duk masu tunanin Arewa fagen yaki ne kawai. Gaskiyar magana shi ne, idan dai kasan wuraren zuwa a Arewa, zaka ji dadinsa.

Dajin yankari na zaune ne a yankin kudu maso tsakiyan garin Bauchi. Gari ne inda akwai furanni, da dabbobin daji da dama, bugu da kari akwai tafki daban daban a garin, Yankari nada matukar ban sha’awa, inda ta kasance wajen bude ido mafi girma a Najeriya tun 1991.

Wadannan hotunan sun bayyana tsananin kyawun dajin Yanakri, musamman kyawun hotunan da aka dauka a kasan ruwa.

 

Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

Wadannan hotunan an dauke su ne a cikin tafkin dajin Yankari. Kyawun hoton nan ya kai matuka. Amma mutum ya tabbata zai iya rike numfashinsa a karkashin ruwa haka kafin ya cimma wannan kyakkyawan yarinyar a kasan ruwa.

Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

A yanzu da ka fahimci tsananin kyawun ruwan nan, toh kada da ka hana ma kanka hutu a wannan jin dadin.

Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

Akwai ababen morewa da dama cikin dajin Yankari, amma fa idan ka cire tsoro a ranka.

Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

Wannan hoton na karkashin ruwa na daban ne; idan za kayi wani bincike daya shafi dabbobin cikin ruwa sai ka zo zuwa dajin Yankari.

Kyawawan hotuna daga tafkin dajin Yankari

Wannan hoton ya nuna asalin halittar Ubangiji. Zancen gaskiya shi ne yankin Arewa wajen zuwa ne duk da matsalar da yankin take fuskanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel