Wani mutum ya nemi auren budurwarshi a dakin jarabawa
Akwai wani abu da kowace mace ke bukata kafin bikin auren ta, wanna kuwa bo komai ba ne illa yadda aka nemi yardar auren ta, lokacin da namiji ze zo da zobe da yadda ze furta maganar.
Samarin Najeriya suna da kitkira, cikin salon neman yardar aure, kuma zasu yi kokarin ganin cewa abun ya zama na musamman da burgewa.
Kamar yadda BelaNaija ya bayyana cewa, wani mutum mai suna Sola ya nemi yardar auren budurwarshi Adeola a dakin jarabawa.
Karanta abunda mutumin ya rubuta. Yace" sannunka Bela, na nemi auren budurwata ranar asabar din da ta gabata a dakin jarabawa, abun ya kayatar ,na neme ta na tsawon kusan shekara 6 kuma na San itace macen da ta dace da ni,abun ya bata mamaki matuka sai sai da taji kamar tayi kuka.
Nagode ma ubangiji saboda ranar da muka hadu, ina cikin masu karanta labarinka ta yanar gizo-shine dalilin da yasa nake son labarina yazo nan dan in kara bata mamaki.
Asali: Legit.ng