Rikicin yan kungiyar matsafa ya lakume rayuka 6

Rikicin yan kungiyar matsafa ya lakume rayuka 6

Rahotannin daga jihar Ribas sun nuna cewa mutane shidda ne suka rasa rayukansu sakamakon wata kazamar rikici data kaure tsakanin wasu kungiyoyin matsafa a jihar.

Rikicin yan kungiyar matsafa ya lakume rayuka 6

Anyi wannan rikicin matsafa ne a kananan hukumomin Ogba, Egbema da Ndoni.

Rikicin ya samo asali ne lokacin da wasu tubabbu yan kungiyar tsafi suka rungumi tsarin afuwa da gwamnatin jihar Ribas tayi musu, kuma suka mika makamansu. Majiyarmu ta shaida mana cewa wasu gungun yan kungiyar matsafa ne mai suna Greenlanders suka suka kai hari a yankin Okposi, na kauyukan Iburu da Obagi.

KU KARANTA: Rikicin kungiyoyin matsafa 2 ya bar mutane 2 a mace

Wata majiya ta karkashin kasa mai suna Rita ta fada ma manema labarai cewa matsafan sun kashe mutane hudu a kauyen Okposi, kafin suka wuce kauyen Obagi inda suka kashe mutum biyu.

Rita tace da misalin karfe 8 na safe ne matsafan suka far ma kauyukan, inda suka dinga harbi a sama, tace suman wandanda aka kashe yan wata kungiyar matsafa ce na mai suna ‘Icelanders’ “harbe harben yayi kamari a ranar lahadi lokacin da Greenlanders suka iso kauyen Okposi suka kashe mutane hudu,” inji ta.

Sai dai jaridar Punch ta ruwaito cewa ana gudanar da bincike akan faruwan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng