Budurwa ta yanke jiki ta fadi ta mutu a hanyar zuwa bayi
Wata budurwa yar kasuwa mai suna Abosede Tumininu ta yanke jiki inda ta fadi ta mutu a ranar Alhamis 22 ga watan Satumba.

Kamar yadda wani ma’bocin kafafen sadarwa na zamani Seun Fasassi ya bayyana, yace Budurwar mai shagon siyar da kaya mai suna ‘Tummie Collections’ na kan hanyar zuwa bayan gida ne lokacin data yanke jiki ta rasu. Ga dai yadda Fasassi ya bayyana ta’aziyyarsa ga mamacin.
“ina kiranta da suna matata, ta fada min miliyan biyu kacal take bukata ta fara gudanar da kamfaninta na siyar tufafi, don ta daina shigo da kaya daga Aliexpress. Bata son mutanen dake kasuwanci a kan yanar gizo, tana bani kwarin gwiwar in ci gaba da kokari a wannan shekarar. Ta nuna min cewa mace ma zata iya yin abinda namiji yayi. Tana da son raha, ga gaskiya. Muna yawan wasa da juna. Gaskiya na karu da ita.
KARANTA:Ma’aikacin filin jirgin sama yayi mumunan mutuwa
Bata tsaya jiran sai gwamnati ta bata aikin yi ba, a’a, ta fara neman kudi da kanta, inda take samun makudan kudade. Ina yawan bada labarinta ga ragwayen mata da na sani. Ta koka kan yadda farashin dala ke kara hauhawa, sai na bata shawarar yadda ake talla a shafin yanar gizo na Facebook.
Da wuya ka samu mace kamarta. A jiya ta rasu yayin da take tafiya bayi, nan da ta fadi ta mutu. Duk wahalan da ta sha wajen neman kudi ya tafi a banza kenan, ita ta fara taya ni murnan sallah
Kamar na kirata a waya jiya, amma sai na manta. Wata kila da na kirata, da kirar ya hanata shiga bayin. Tumininu ta tafi. Muna kaunarki, amma Ubangiji yafi kaunarki. Ina addu’ar Ubangiji ya baiwa yanuwanta hakuri. Da fatan zaki samu hutu a makwancin ki. Zanyi matukar kewanki.
Asali: Legit.ng