Dalilai 7 da Arewacin Najeriya ba sa so Najeriya ta rabu

Dalilai 7 da Arewacin Najeriya ba sa so Najeriya ta rabu

- Kasar Najeriya kasa ce wadda take a yammacin Afrika                                      

- Hanyoyin yin safara na ruwa suna yankin kudancin Najeriya                            

-Yawancin masu ilmin Boko suna yankin Kudu

Najeriya kasa ce wadda take a yammacin nahiyar Afrika, wadda take da fadin kasa na fadi da tsawon kilo mita 923,768, kasar Najeriya tana da iyaka da kasar Chadi ta gefen Arewa maso gabas, iyakar kasar kum da Kamaru tana ta Arewa maso gabas, daga iyakar ta ta kudu kuma tayi iyaka da Atlanta, tayi iyaka da kasar Niger ta yankin arewa maso kudu, iyakokin Najeriya da Chadi da kuma Najeriya da Kamaru akwai lokacin da kowa ke gadarar gurin shi ne, har y kawo rikici tsakanin iyakokin.

Kasar Najeriya tana da yarurruka fiye da 50, amma yarurrukan da suka fi rinjaye su ne Hausa/Fulani masu kaso 28%, sai yaren Yarbanci wanda yake da kashi 21%, sai yaren Inyamuranci/Ibo wanda ke da kaso 18% na yarurrukan.

Hausa/Fulani suke zaune a arewacin Najeriya wanda ya hada da jahohin Sokoto, Adamawa, Kano, Jigawa, Bauchi, Nasarawa da sauransu, sai Yarbawa da suk mamaye yankin kudun masu yamma na kasar wanda ya hada da jahohin Oyo, Ondo, Osun, Ogun da sauran su, sai Inyamurai/Ibo wadanda suke yankin Kudu maso gabashin kasar masu jahohin da suka hada da Imo, Abia, Anambra, Enugu da sauran su.

Dalilai 7 da Arewacin Najeriya ba sa so Najeriya ta rabu

Yaren da ake amfani da shi na kasar a gwamnatance shine yaren turanci, sakamakon turawan mulkin mallaka da su ka raini kasar.

Najeriya tana da addinai da mabiya, amma addinai da suke da yawancin mabiya sune addinin musulunci da Kiristanci sai yan kalilan masu yin addinan gargajiya, kusan kaso 90 na mutanen da Ke arewacin Najeriya suna bin addinin Musulunci, sai kashi 85 na mazauna kudan cin da Ke bin addinin kiristanci, addinin musulunci yayi karfi a arewa a dalilin jahadin Shehu Usmanu Danfodiyo, shi kuma Kiristanci yana da karfi a yankin saboda fara saukar Mishinari a yankin na kudu.

Kasar Najeriya tan da jahohi 36 da babban birnin tarayya Abuja, Najeriya kasa ce mai arziki wadda ta dara kowacce kasa a Nahiyar Afrika saboda suna da sukayi na samar da man fetur, Kwallin kura, Roba, Zinare, Noma da sauran su.

Dalilai 7 da Arewacin Najeriya ba sa so Najeriya ta rabu
Taswirar Najeriya

Wadan nan dalilan guda 7 a kasa sune suka sa arewacin Najeriya ba sa son Najeriya ta rabu.

1. Ilimin Boko

Ilimin Boko yana 1 daga cikin dalilan da yan arewa basa son a rabu, saboda yana da karfi a yankin kudu a dalilin fara saukar turawan mulkin mallaka a yankin, wanda a lokacin arewacin Najeriya suna ganin kamar wani ra'ayi ko akida za'a tura masu, wanda a halin yanzu arewacin suna gajiya da ilimin na boko.

2. Kasuwanci

Duk da yake kusan cibiyar kasuwanci ta Najeriya tana Kano arewacin Najeriya, amma kudancin Najeriya su suka fi kasuwanci, garuruwa kamar kamar Aba, Lagos, Onitsha, Ibadan ana huldodi na kasuwanci kuma ana kawo wasu abubuwa da babu su a Kano, wannan shima ze Iya zama dalili,

3. Masana'antu ko Kamfanoni masu zaman kansu

Yawancin ma'aikatu da Kamfanoni suna yankin kudancin kasar, kuma suna cikin abubuwan da suka habaka yankin, wanda in ka lura babu su a arewa, koma akwai to basu da yawa ko basa aiki.

4. Man Fetur

Rashin man fetur shima ze Iya zama babban dalili saboda shine kusan abinda kasar ta dogara da shi, dan haka in aka raba kasar, arewacin Najeriya zasu rasa tudun dafawa.

5. Hanyoyin safara na ruwa

In zaka yi la'akari yawancin hanyoyi da ake shigowa da kaya ko fita da su ta ruwa suna yankin kudan cin kasar, wanna shin abun da y daga Kasuwancin su da samun kudin shiga na yankin, in kasar ta rabu wannan ze kawo babban Kalu bale a yankin Arewa.

6. Samar da tsintsaye da kayan marmari

Tsintsaye da kayan mamari da abincin tsintsaye duk yawanci ana samun sune a kudancin kasar, wanda kuma wadan nan ababe sun zama abun amfanin yau da kullum, wannan kadai ze Iya kawo cikas a yankin na Arewa.

7. Kirkire-Kirkire

Yawancin yan Arewa sunfi yin noma su aika amfanun gonan a yankin Kudu, su kuma su sarrafa ta hanyoyi da dama, kuma har yau kudan cin Najeriya suna amfani da kayan al'ada wanda arewacin  wasu suka watsar, wannan ma ze iya zama na kasu ga Arewa in kasar ta rabu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng