wannan kerkecin yanayin abubuwan mamaki irin na mutane

wannan kerkecin yanayin abubuwan mamaki irin na mutane

Zaki da damisa dai abun tsorone, amman idan kuka ga girman wannan kerkecin, zaku iya zurawa da gudu. Ka kaddara ka gamu da wannan katon abun a daji!

Akwai dai labarai da yawa akan kerkeci, mutane suna kwaikwayon yin ma'amala dasu a wurare da dama saboda irin hallitar su domin kuwa sukan ba mutane tsoro. Amman wannan managarcin kerkecin ya baiwa mutane mamaki, musamman idan akayi la'akari da girmansa da kuma irin sabon da yayi da mutanen da yake tare dasu.

wannan kerkecin yanayin abubuwan mamaki irin na mutane

Wannan mutumin ya samu damar yin abota da kerkeci. Yakansa su kwanta kasa, idan wani daga cikinsu ya mike, kamar yadda akeyima karnuka. Zakuyi mamaki idan kukaga irin girmanta!

Kerkecin dai sunfi zama a wani kebabben waje inda suke da shuwagabannin su masu kula dasu. Wannan mutumin yana daya daga cikin su (Bawai dan yana wasa dasu ba!) domin namun dajin suna girmamashi kuma sun yarda dashi. suna amsan abinci a wurinsan kuma idan suka tashi saisu dunga kokarin sauka akan kafadarsa.

wajan nasu yanada kyawun gani kuma masu yawon bude ido zasuji dadin wajen, musamman idan suka daukesu hotuna sannan su shiga cikin shingen da akayi musu kai tsaye.

Haka kuma, yawancin mu zamuji tsoro kwarai da gaske musamman idan mukaga irin wannan abun a cikin daji alokacin da muke mu kadai! kerkeci yakanyi girma sosai kuma yakan bada tsora kwarai. Amman kuma zai iya zama abokinka sannan kana iya sabawa dashi.

Abin mamaki!

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng