Idan Ango da Amarya suna da kyau
Andai ce soyayya kamar iska ce, bamu ganin ta saidai mujita a jikin mu, ma'aurata.
Haka kuma soyayya kamar hikayace. Kamar yadda akace a Bible. Ka zama mai gaskiya da yawa. Cris da Odiola sun kai wani mataki na tarayyar da sukeyi. Sun hadu inda sukayi bikin murnan soyayyarsu kuma suka nuna ma duniya cewar sun shirya domin su sami kyawawar zuri'a wanda zasu kara dankon soyayya da kyauna a tsakanin su.
Hotunan sun sanya jama'a sunyi maganganu sama da dubu. Idan har akazo maganar soyayya, to zaiyi wuya a iyayin cikakken bayani akansa tare da kuma yadda akejinsa a jiki.
Wannan Ango da Amarya sun bayyana soyayyar su, inda suka sanya hotunan su daya nuna tsantsar soyayyar da suke yima junan su. Wanda za'a iya cewar basu da matsala a tsakaninsu, inda akaga suna kwalliya iri-iri, suna kuma taimakon junansu, sun yarda da junan su kuma dukkanninsu sun sami muhalli a zuciyoyin junansu.
.
Hotunan nasu sun nuna soyayyar su a zahirance, haka kuma suna cikin murna da zaman walwala a auren su. Kalli dai sauran kyawawan hotunan nasu da suka dauka kafin auren su.
Asali: Legit.ng