Sarki Muhammadu Sunusi II ya gana da Fafaroma
Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II ya gana da Fafaroma Francis a garin Asisi na kasar Italiya, tare da sauran shuwagabannin addinai su 450 a ranar da aka ware don yi ma Duniya addu’ar zaman lafiya.
Taron addu’ar da aka shirya shi kwanaki uku ne, inda ya fara daga ranar litinin 20 ga watan satumba, kuma an shirya shi ne domin tara shuwagabannin addinai daban daban don yi ma Duniya addu’ar zaman lafiya.
Gidan rediyon kasar Vatican ta bayyana cewa Fafaroma ne ya jagoranci zaman rufe taron na karshe da aka yi ma taken: ‘kishin neman zaman lafiya, tattaunawa tsakanin addinai da al’adu’. An ruwaito Fafaroma yana cewa “mun zo garin Asisi ne domin neman zaman lafiya. Muna dauke da nauyin mutane da dama, muna bukatar zaman lafiya, kuma muna son ganin zaman lafiya.”
A yayin jawabinsa, Sarki Muhammadu Sunusi yace “muna bukatan yin addu’ar zaman lafiya fiye da komai, saboda zaman lafiya wani kyauta ne daga Allah, kuma mu hakkin mu ne mu neme shi, mu rungume shi, tare da gina shi cikin ikon Allah”
KU KARANTA: Hotunan Sarkin Kano Da Matan Shi Da Yaran Shi
Rahoton ya ruwaito Fafaroma yana jawabi yayin da yake ganawa da wasu darikun addinin Kirista daban daban, Fafaroma yace “tun kafin a gicciye Yesu, badadin Ubangiji, an bukaci Kirista da mu tuna soyayyar Ubangiji, kuma mu yada soyayya a cikin Duniya, a lokacin da aka gicciye shi, an canza mummuna zuwa kyakkyawa, mu kan mu a matsayinmu na almajiran shi, ana bukatar damu maido da iskar soyayya cikin duniya.
“An samu ruwa na bubbuga daga gefen Yesu, alamar ruhi mai bayar da rai kenan, saboda so da kauna zai watsu daga garemu. Shekaru talatin da suka wuce, Fafaroma John Paul na II yace “zaman lafiya wajen aiki ne, mu bari kowa ya shigo, ba wai sai kwararru ba kawai. Hakkin samar da zaman lafiya na kan kowa.
“Don haka ya kamata mu dauki wannan nauyi, mu tabbatar ma kawunan mu, cewa zamu zauna tare kuma mu kasance masu gina zaman lafiya da Ubangiji ke so mana, wanda kuma jama’a ke matukar bukata.”
Asali: Legit.ng