Wata yar shekara 62 ta samu ciki a kasar Spain

Wata yar shekara 62 ta samu ciki a kasar Spain

Abun al'ajabi baya karewa, wasu abubuwan sukan cigaba da ba mutane mamaki ta fanni daban-daban. Kamar yadda masana ilmi ke cewa aukuwar wasu abubuwa na kalubalantar bayanai na kimiyya subar mutane da mamaki.

Idan aka zo gurin cimma buri a duniya, wasu mutane kan samu kadan, wasu kuma su rasa, basu da Imani kuma basu yadda da kaddara ba.

Wata yar shekara 62 ta samu ciki a kasar Spain

Shiyasa wasu sukan hakura a fagen fama, wasu kuma sun kan nema suke mutuwa, in dai da rai da buri, ya danganta da abun da aka tsinci kai a ciki, abubuwa zasu iya canzawa lokacin da baka zata ba.

Da zarar kaddara ta fada ma wasu, sai suyi tunanin rayuwarsu ta zo karshe, wasu kuma sukan yi nasara da zarar sun fara wani abu.

Labarin yar shekara 62 ze kara karfafa mak guiwa da kara yarda ga Allah, Wai shin a duniya wa yake da yakinin sannin ayyukan manyan yan kimiya.

Lina Alvarez yar kasar Spain ce, tana neman haihuwa bayan yi mata aiki da akayi. Yar shekara 62 ta samu ciki bayan ta wuce lokacin haihuwa da shekara 20, duk da yake cikin ba na farko bane, amma abin mamaki ne a ce mace mai shekarunta tana tsammanin zuwan sabon jariri.

Alverez dai cikinta ya kai wata 8 kuma ana tsammanin zata haihu wata oktoba, duk da yake wannan ba ita ce haihuwar ta ta fari ba, tana da yara maza guda 2, babban kuma yana bukatar kulawa saboda likitoci sun sun bata mai kai kafin haihuwa, karamin shekarar shi 10, shi kuma babban yaba karamin shekara 17.

Tace abin kaddara ne kuma abun mamaki ne, mafi yawan cin karatun likitoci sun nun cewa ba ze yiwu a haihu a Shekarun ta ba duk da tana bukatar haka, duk da rashin kwarin guiwar da akai ta bata, ta hadu da likitan mata da yake shirye da taimakon ta.

Ya kammala gwaje-gwajen sa kuma yana da kudurin taimaka mata, yace ingancin aikin samun haihuwa kaso 6%, zaka yi mamakin mai shekara 62 zata samu ya ta 3.

Bata damu da abinda ake fada ba Wai zata zama kaka kuma uwa yayin da jaririyar ta ta zata cika shekara 30. Abun ja jawo hayaniya a kasar Spain inda ake cewa be kamata a yi aikin ba in za'ayi la'akari da shekarunta, ita kuma bata damu da haka ba lokacin da ta matsu ta ga yar ta ta 3.

Asali: Legit.ng

Online view pixel