Abinda ta samu a gasashshiyar kaza ya tayar mata da hankali
Kana kaunar gasassar Kaza?Rose Mary tana kaunar gasassar kaza itama.Abinda ya faru da ita ya bada mamaki matuka.
Hoton kwanon abincin da ta saya da abin kaicon da tagani ya samu sakawa a dandalin sadarwa kuma kimanin mutane 140,000 suma sun saka dan sauran jama'a su gani! Ta fara cin kazar har ta ci kusan rabi sai gashi taga wani abu mai daga hankali.
Ta dauko ta saka a baki inda taji ta tauna kai, ba ma Wai kan kaza ba, abin mamaki kan gasasshen bera a kwanon abincin ta kuma abin ban haushin bata gani ba sai da saka a baki tagane.
Tayi mamaki, kuma taji kyama, tayi kokarin daukar hotuna na kwanon abincin da abin da ta samu a ciki, abu na gaba da matar tayi shine ciwon ciki da amai. Taje gurin ma'aikata gidan abincin dan tayi karafi, amma sun ce wani sashe ne na kaza ba bera ba.
Mutane da yawa sunyi tsokaci a dandalin sadarwa cewa wannan ba shine dalilin da ze hana mutum cin abinci ko nama a gidan cin abinci ba, kawai Tsoron su suci abinda ze Iya narkewa a cikin su.
Asali: Legit.ng