Wani ya bayyana yadda ya kama kaninsa da matar fasto
- Wani mutum ya bayyana yadda ya shigo gida ya tarar da kaninsa na zina da matar malamin cocinsu
- Yayinda ya watsa wannan labara a shafin sada zumuntarsa, mutumin yace abin ya basa tsoro, yace ya dawo daga wajen aiki sai ya shiga cikin daki ya tarar da matar fasto da kaninshi zindir haihuwar uwarsu
Yace:
“Na ga wani abinda ban taba zato ba a rayuwata, da ranan nan, na kama matar faston mu, wacce nike ganin girmanta sosai, haihuwar uwarta tare da kani na. Iyayenmu sun je kauye sun bar mu biyu a cikin gida.”
KU KARANTA:Allah ya kyauta! Wani yayi wa yar’uwar sa fyade
“Ina da digri amma ina koyarwa a wata makarantan Sakandare. Na bar gida da safe kuma in dawo da karfe 4 na yamma. Amma yau ba haka bane, saboda mun yi wani taro malamai sai muka tashi da wuri. Na shiga gida, kawai sai na gan su zindir haihuwar uwarsu.”
“Abin ya bani mamaki. Nayi iwun sunan kanina. Amma na tafi mashaya yanzu saboda in natsu. Ban ma san abinda zanyi ba, ban ma gane abinda ya faru ba ko kuma yaya ya faru.”
Asali: Legit.ng