Soji da yan Boko Haram sunyi batakashi a Fatori

Soji da yan Boko Haram sunyi batakashi a Fatori

Yan Boko haram da dama da sojin rundunar Joint Multinational Task Force (MNJTF) sun rasa rayukansu a wata batakashi da akayi a Mallam Fatori a jihar Borno a ranan Talata, 21 ga watan Satumba.

Associated Press ta ruwaito cewa yan kungiyan Boko haram sun sanya a shafin sada zumuntarsu cewa sun kashe sojin MNJTF 40 amma ddai ba’a tabbatar da hakan ba har yanzu.

Soji da yan Boko Haram sunyi batakashi a Fatori

“Daular islama ta yankin Afrika ta kudu ta hallaka wata rundunar sojin afrika a garin Malam Fatori. Har yanzu dai hukumar sojin Najeriya bata fadi komai akan zancen ba kuma ba’a san adadin wadanda suka mutu ba.AP ta rubuta.

KU KARANTA: Boko Haram sun kai hari a Borno

Amma dai, hukumar Sojin Najeriya ta tabbatar da cewa anyi wata batakashi a wata jawabin da kakakin sojin ya bayyana, Kana Sani Kukasheka Usman a ranan laraba, 21 Satumba.

Jawabin ta tabbatar da cewa yan boko haram din sun dan bada wuya amma an kashe da dama daga cikin su a batakashin.

“A cigaba da Operation GAMA AIKI, rundunar Operation LAFIYA DOLE da MNJTF suka kwato garin Malam Fatori a jihar Barno bayan wata batakashi da akayi.

“Amma,yan ta’addan sun sami Karin karfi a boda Nijer. Shi yasa rundunar suke jin dadi. Sun kashe da dama daga cikin yan boko haram din amma daga baya suka koma, za’a cigaba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel