Najeriya zata shawo kan matsalan Neje Delta ba dadewa ba

Najeriya zata shawo kan matsalan Neje Delta ba dadewa ba

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari yace Najeriya na dauka matakai wajen shawo kan masalilon Neja Delta

- Shugaba Buhari ya tabbatar da hakan ga Shugaba Obama a wata tattaunawan kasa da kasa da sukayi a gefe daya wajen taron gangamin majalisan dinkin duniya da akayi a Newyork

- Ya jaddada cewa gwamnatinshi ta dau ragamar muki ne akan alkawura guda 3, tsaro, yaki da rashawa, da kuma farfado da tattalin arziki

- Shugaba Buhari ya taya Obama murnan shirin sau kadaga mulkin da yake shirin yi

Najeriya zata shawo kan matsalan Neje Delta ba dadewa ba

Shugaba Muhammadu Buhari yace Najeriya na daukan matakai na tabbatar da cewa an shawo kan matsalolin yankin Neja delta wacce ta janyo tabarbarewan tattalin arzikin kasa.

A wata jawabin da mai Magana da yawun shugaban kasa, Femi Adesina ya bayyana: “Muna daukan matakai nagaske akan sanin kungiyoyin yan bindiga nawa akawi, shugabannin su ,inda suke aiki da kuma mun nemi hadin kan su ma. Ba da dadewa ba ,za’a shawo shan komai.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne a ranan Talata, 20 ga Satumba ga Shugaba Obama a wata tattaunawan kasa da kasa da sukayi a gefe daya wajen taron gangamin majalisan dinkin duniya karo na 71 da akayi a New York.

KU KARANTA: Taron UN: Bambancin Tafiyar Shugaba Buhari da ta Shugaba Jonathan

Yayinda yake mikin godiyan sa ga gwamnatin Amurka da taimakon da ta bada wajen tsaro ta hanyar bayar da makamai da kuma horo ga rundunar sojin najeriy,da kuma ayyukan lekan asiri wanda ya taimaka wajen dukufar da Boko Haram a yankin arewa maso gabas, shugaba Buhari yace kasar Amurka na da daman taimakawa wajen tallafi ga mutanen yankin.

Shugaba Buhari yace daminar wannan shekarar tayi armash, ana sa ran girban yabanya sosai kuma “Najeriya na hanyar ciyar da kanta ada kuma yin amfani da dalolin biliyoyin kudin da shigo da abinci domin yin wadansu abubuwa.

Ya jaddada cewa gwamnatinshi ta dau ragamar muki ne akan alkawura guda 3, tsaro, yaki da rashawa, da kuma farfado da tattalin arziki kuma babu abinda zai sa su daina yin hakan.

Shugaba Buhari ya taya Obama murnan shirin saukadaga mulkin da yake shirin yi

Bada amsa, shugaban kasan Amurka ya sifanta shugaba Buhari a matsayin mutum mai mutunci da tsoron Allah, yace: “Mun amince da gwamnatin ka. Kana fuskantan matsaloli,amma wannan gwamnati na shirin taimakawa a kankanin lokacin da ya rage mata . ka ci nasara sosai wajen dukufar da boko haram kuma wannan ya faru ne saboda shugabancin ka.”

Shugaba Obama ya mika hannun abota ga Najeriya wajen karasa kawar da boko haram, shawo kan matsalan Neja delta,wanda zai taimakawa samun mai kuma farfado da tattalin arziki, tallafi a yankin arewa maso gabas,kwato satattun kudade da kuma farfado da tattalin arziki.

Shugaba Muhammadu Buhari wanda ke birnin Newyork yanzu ya bayyana ma shugaban kasan Afrika ta kuma, Jacob Zuma, cewa tsaro yanzu ya samu a najeriya kuma yana tabbatar ma masu sanya hannun jaari da kuma masu niyyan saw a cewa rayuwan su da dukiyoyin sun a cikin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng