Barawo yayi sata a ofishin yan sanda

Barawo yayi sata a ofishin yan sanda

Rundunar yansandan jihar Legas sashin kai dauki (RRS) sun kama wani mai suna Deji Ayoola da ake zargi da yi ma pasinjojin mota sata a Legas.

Barawo yayi sata a ofishin yan sanda
Barawo Ayoola

Jaridar Punch ta ruwaito yan sanda sun kama Ayoola mai shekaru 28 ne a Ojudu na unguwar Berger bayan ya sace ma wani pasinja mai suna Ayodele Akerele kudadensa dake kulle a cikin asusun fata (wallet) a aljihunsa.

Bayan an kammala binciken sa a ofishin yan sanda, sai kwatsam ya sace ma wata jami’ar yan sanda N1200 wadanda suka fado daga aljihunta yayin da take kokarin ciro wayanta daga aljihun nata.

KU KARANTA: Dubi yadda sojoji suka horar da barawo

A lokacin da yake ma yansandan magiya yayin da ake gudanar da binciken, Ayoola ya danganta halin nasa da sharrin shedan, inda aka jiyo shi yana cewa “wannan sharrin shedan ne”

Jami’an hulda da jama’a na rundunar yansandan jihar Legas Dolapo Badmos ya tabbatar da kama mai laifin, inda yace sun mika shi zuwa ga hukumar kula da laifukan muhalli da laifukan na musamman na jihar legas don su gurfanar da shi gaban kuliya manta sabo.

A wani labarin kuma, jami’an rundunar yansandan jihar Legas sun kama wasu mutane uku yan kugiyar tsageru. Wadanda aka kama su ne Sylvester Ebi, Preye Munbo da Isaiah Ikechukwu, ana zargin su da kasancewa yayan wata kungiyar tsageru data addabi al’ummomin Iba da Igando na jihar Legas, rundunar yansandar tace ta kama su ne yayin wani samame data kai a kauyen burai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel