Hanyoyin maganin cin hanci da rashawa a Nigeria

Hanyoyin maganin cin hanci da rashawa a Nigeria

Tsohon Shugaban hukumar EFCC Nuhu Ribadu, ya bayyana wasu hanyoyi da za bi domin maganin cin hanci da rashawa da ya addabi kasar

Ganin yadda ake maganin kaba, kai na dada kumburi dangane da matsalar cin hanci da rashawa a Nigeria, a ranar Litinin 19 ga watan Satumba Nuhu Ribadu ya bayyana wasu hanyoyi 12 da za a iya maganin matsalar.

Hanyoyin maganin cin hanci da rashawa a Nigeria
Nuhu Ribadu, Shugaban hukumar EFCC na farko

Shugabanci nagari: Muddin ba za a samu jagoranci nagari ba, da kuma yin hukunci na ba sani, ba sabo ba, kasar nan za ta dade ba ta yi maganin da matsalar ba.

Yabawa aikin gaskiya: A rika karrama wadanda suka nuna hali nagari da gaskiya a mataki na kasa, al’umma kuma ta daina girmama masu dukiyar haram.

Aiki da kasafin kudi: Duk wani kudi da gwamnati za ta kashe ya zama yana cikin tsarin kasafi, duk wani kudi da za kashe a wajen tsarin ya zama laifi, gwamnati kuma ta soke kashe kudin debi-da-kanka da sunan tsaro.

A yi komai a bayyane: A daina kumbiya-kumbiya a ayyukan gwamnati daga kasafin kudi zuwa ga bayar da kwangiloli har zuwa daukar ma’aikata.

Kimiyya da Fasaha ya zama jigo: A yi amfani da kimiyya da kuma fasahar zamani wajen sayen kayyakin domin bayar da damar yin komai a bayyane tare da bibiyarsa a zamanance.

Daukar da kudi a hannu: Ya kamata a takaita ko kuma a daina tsarin hada-hadar cinikayya kudi-hannu a gwmnatance. A koma amfani da hanyar zamani na biya da kuma karbar kudade wacce babu kumbiya-kumbiya, kuma za a iya bibiya.

A magance magudin zabe: Ya kamata a yi maganin cin hancin da rashawa ta hanyar magudin zabe, domin har idan a ka ci gaba da zaben shugabanin ta wanna hanya, zai yi wahala a yi maganin cin hanci da rashawa.

‘Yan jarida da kuma kungiyoyi su sa ido: A karfafi kafofin yada labarai da kuma kungiyoyin al’umma masu zaman kansu su sa ido kan al’amuran kudi. A kuma karfafi masu tonon silili tare da kare su.

A rage matakan aiki: Rage matakai ko tsani na gudanar da aiki a gwamnatance saboda cikas, hakan kuma zai hana neman a  bayar da na goro a yayin aiki

A janye tallafi: Tallafi ta kowacce fuska a gwamnatance na haifar yanayin cin hanci da rashawa ga masu cin gajiyarsa da kuma masu amfana da shi, yana da kyau a cire shi baki dayansa.

Ilimin sanin ya kamata: Ya kamata a ilmantar da ‘yan kasa kan sanin dai dai, ta haka ne za su iya sanin abin da ya dace da kuma akasin hakan.

Kudiri: Kowa ya kudiri aniyar kin bayar da cin hanci, idan har kowa ya tsaya kan bakansa na kin bayarwa, wata rana sai an rasa mai karba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel