Wani mutum ya kashe 'yarsa bayan data kubuta daga ciwo

Wani mutum ya kashe 'yarsa bayan data kubuta daga ciwo

Wani mutum ya kashe karamar 'yarsa wacce ta warke a sanadiyar fama da ciwon daji, saboda kishi.

Wani mahaifi dan shekara 25 mai suna Ryan Lawrence, an kamashi da laifin kashe 'yarsa, 'yar shekara 1 a duniya mai suna Maddox, wacce tayi fama da ciyon daji na ido.

Wani mutum ya kashe 'yarsa bayan data kubuta daga ciwo

Haka kuma, an bayyana cewar Lawrence ya daki yarinyar ne da abun buga Baseball, asakamakon abunda aka kira da bakin ciki, saboda kulawar da yarinyar take samu daga wajen mutanen da suke kulawa da ita.

Wani mutum ya kashe 'yarsa bayan data kubuta daga ciwo

Acewar rahoton, Lawrence ya sace yarinyar sa inda ya kaita wani waje daban a Onondaga Country a New York, inda anan ne yayi mata duka da wani abun buga Baseball, wanda daga karshe kuma ya sanyama gawar nata wuta.

Abun dai ya faru ne a watan Afirilu, haka kuma, an kama Lawrence bayan da 'yan uwansa suka kai sanarwar bacewar yarinyar a wajen 'yan sanda.                           Inda akayi nasarar kamashi a washegarin ranar, a inda akaga gawar Maddox's bayan awa 12.

Wani mutum ya kashe 'yarsa bayan data kubuta daga ciwo

Acewar binciken da 'yan sanda sukayi, Lawrence ya roki Allah daya nuna masa wani alama da zai hanashi kashe yarinyarsa, inda yace " Allah idan bai kamata na kasheta ba, to kasa nayi kuskure, kuma batasa nayi kuskure ba" sai kawai ya kashe ta.

Lawrence wanda za'a yanke ma hukunci a watan gobe, wanda bai wuce shekara 25 ba aduniya, zai iya fuskatar hukunci zama a gidan yari na iya tsawon rayuwar sa.

Allah ya kyauta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng