Gwamnan Neja ya roki gwamnatin tarayya kan gyaran hanya

Gwamnan Neja ya roki gwamnatin tarayya kan gyaran hanya

Gwamnan jihar Neja Abubakar Sani Bello ya roki gwamnatin tarayya da ta kammala aikin da ta fara kan hanyar Suleja zuwa Minna na raba shi zuwa tagwayen hanyoyi.

Gwamnan Neja ya roki gwamnatin tarayya kan gyaran hanya

Gwamnan ya mika kokon bararsa ne yayin da yake zagayen duba aikin hanyar ta bangare kauyen Bonu na karamar hukumar Gurara, gwamnan ya bayyana damuwarsa dangane da halin da hanyar ke ciki, yace ya kamata gwamnati ta duba hanyar da idon basira.

“Duk da cewa hanyar gwamnatin tarayya ne, munyi iya kokarin mu wajen gyaransa a matsayin mu na jiha. Na bada umarnin gyaran hanyar, amma saboda yawan ababen hawa dake bin hanyar da kuma dadewar hanyar, gyaran da aka yi bai dade ba ya lalace.

KU KARANTA: Yadda matasa masu fushi sun kai hari a gwamna

“Ya kamata gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatan ayyuka da ta dauki aikin da muhimmanci. Asali, awa daya da mintuna 30 zai kaika Abuja daga Mina, amma yanzu sai ka kwashe awanni 3,” inji Bello.

Bello ya kara kokawa kan tsawon lokacin da ababen hawa ke batawa a kan hanyar, tun bayan fara aikinta sama da shekaru 6 da suka wuce.

Gwamna Bello yace gwamnatin jihar Neja tayi iya bakin kokarinta wajen gyara hanyar, amma hakanta bai cin ma ruwa ba. Ya bukaci gwamnatin tarayya data dauki matakin gaggawa wajen gyaran hanyar, ta hanyar samar da kudi daga kasafin kudi don yan kwangila su koma bakin aiki.

Sai dai, jami’in kamfanin dake gudanar da aiki Paolo Campanella yace: “Karancin kudi yasa aikin ke tafiyar hawainiya,  kashi 20 na kudin aikin kadai aka biya mu don gudanar da aikin. Naira biliyan 34 ne jimillar kudin aikin, amma a cikin shekaru 6 da aka fara aikin, naira biliyan 6 kacal aka bamu.”

Campanella ya yaba ma gwamna Bello saboda nuna damuwa da yayi da hanyar, yace: “Kamata yayi mu kammala aikin nan a watanni 30, an bada kwagilar sashin na farko a shekarar 2010, kuma ya kamata mu gama shi a watan yulio na 2013, amma yanzu lokacin ya wuce, don haka sai an kara wasu shekarun kafin a kammala.”

“Sai sashi na II da aka bada kwangilarsa a watan feburairu na 2015 duk da cewa ba’a biya kudin fara aiki ba, sakamakon basussukan da muke bi, don haka ba zamu cigaba da aikin ba,” inji shi.

Haka zalika, tsohon shugaban rikon karamar hukumar Gurara, Yakubu Garba da hakimin Bonu Alhaji Ibrahim Baba sun gode ma gwamnan don koakrin da yake yi don ganin an gyara hnayar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng