Buhari, Osinbajo, da wadansu sun amshi N2.29 biliyan

Buhari, Osinbajo, da wadansu sun amshi N2.29 biliyan

- Rahoton baya-baya kan kudaden ma'aikatan gwamnati na nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari kadai ya cancanci albashi alawus na wahala

- An takaita alawus na wahala a matsayin 50% na kayyadajen albashi ga shugaba da mataimakinsa

Buhari, Osinbajo, da wadansu sun amshi N2.29 biliyan

Wani rahoto na kwanan nan kan albashin ma'aikatan bangaren zartaswa na gwamnati na nuna cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa Yemi Osinbajo kadai ke amsar alawus na wahala.

KU KARANTA: Siyasa da tattalin arzikin Arewacin Najeriya bayan yanci kai a 1960

Rahoton, bangare ne na kudaden ma'aikatan gwamnati da hukumar tantance kudaden ma'aikatan gwamnati (RMAFC) ta amince dasu wanda mujallar Economic Confidential, ya wallafa ya nuna cewa shugaba Buhari da mataimakinsa  Osinbajo kadai ke amsar kashi 50% na albashinsu a matsayin alawus na wahala.

Rahoton na nuna Shugaba Buhari na amsar tsantsar albashi mai yawan N3.51 miliyan a shekara, Osinbajo na amsar N3.03 miliyan a shekara yayin da ministoci, sakataren gwamnati da shugaban ma'aikata ke amsar N2.02 miliyan a shekara. Wannan na nuna cewa shugaban da mataimakinsa na amsar N1.75 miliyan da N1.52 miliyan a matsayin alawus na wahala.

Rahoton kuma ya nuna cewa kudaden da aka biya shugaban, mataimakinsa da kuma sauran manyan ma'aikatan bangaren zartaswa a shekara ya kama N2.29 biliyan.

Rahoton, a cewar mujallar ya fito lokacin da gwamnatin tarayya ke kaddamarda kampen dinta na canza ma 'yan kasa dabi'u koko 'Change begins with me.''

Asali: Legit.ng

Online view pixel