Jami’an rundunar sojan ruwa sun motsa jiki
Rundunar sojan ruwa ta kasa ta gudanar da faretin jijjiga jinni karo na uku a birnin tarayya Abuja.
Makadan rundunar sun yiwa jami’an rundunar rakiya yayin da suke gudanar da motsa jikin, wanda hakan ya kara ma atisayen armashi.Jami’an sun somo atisayen ne daga filin fareti na barikin soja na Mogadishu da misalin karfe 6 na safe zuwa barikin soja na Neja, kuma suka sake komawa barikin Mogadishu.
KU KARANTA: Rundunar sojan ruwa tayi bajakolin jiragen yaki 30 kirar Najeriya
Legit.ng ta lura da cewa kusan kowanne matsayin sojan rundunar akwai shi cikin masu atisayen, har ma da wakilan yan yiwa kasa hidima. An jiyo hafsoshin soja tare da kananan sojoji suna wake cikin raha da annushuwa yayin da suke gudanar da atisayen. Yayin da yake yi ma yan jarida karin haske.
Wakilin babban hafsan rundunar sojan ruwa ta kasa Rear Admiral Ogunlowo yace atisayen da suka gudanar nada matukar mahuhimmanci ga jami’an rundunar, ya jaddada amfanin atisayen ga lafiyar su, daga nan ya tabbatar da cewa rundunar zata cigaba da gudanar da atisayen lokaci zuwa lokaci.
A wani labarin kuma rundunar sojan ruwa ta cafke shugaban wata kungiyar tsageru-Bakassi strike Force, mai suna Uduak Etim Thompson, an kama Thompson ne tare da wasu yan kungiyar guda hudu a maboyarsu dake garin kalaba.
Asali: Legit.ng