Wasu 'yan siyasa da su ka yi kaurin suna

Wasu 'yan siyasa da su ka yi kaurin suna

Ga wasu ‘yan siyasa da ake ganin sun fi kowa shiga ka-ce-na-ce a Najeriya saboda kaurin sunan da suka yi a maganganunsu

Ayodele Fayose

Wasu 'yan siyasa da su ka yi kaurin suna
File photo: Governor Fayose flagging off construction of flyover in Ado-Ekiti

Gwamnan jihar Ekiti Ayo Fayose baya bukatar bayani ga duk wanda ya ke sauraron kafofin yada labarai. Gwamman da wasu suka yi masa da lakabi da ‘fitinanne’ dan jam’iyyar PDP ne, ya kuma sa gwamnatin Buhari a gaba da suka, kazafi, da kuma kage, duk da sunan adawa, EFCC ta kuma sa shi a gaba da zargin cuwa-cuwa.

Cif Femi Kayode  

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama a zamanin mulkin Obasanjo, kuma daya daga cikin jigon yakin neman zaben Jonathan a shekarar 2015, Osasanjo ne ya dawo da shi Najeriya daga Amurka inda ya ke “tukin tasi” a cewar wasu, shima a duk lokacin da ya bude bakinsa sai ya yi furucin da zai wasu su yi Tir, wasu kuma na madallah.

KU KARANTA KUMA: https://hausa.legit.ng/970389-fayose-na-cigaba-da-rusa-gidjen jama'a

Balarabe Musa

Tsohon gwamnan jihar Kaduna a karakshin jam’iyyar PRP ta Aminun Kano jamuiriya ta biyu lokacin mulkin Shagari, a duk lokacain da Balarabe ya bude baki ya yi wata magana sai ka ji a gari ya dauki dumi, saboda akidarsa ta ‘yan gurguzu da kuma a cewarsa, talakawa ne a gabansa. Ba ya jam’iyya mai mulki ko ta adawa.

Wasu 'yan siyasa da su ka yi kaurin suna
Ministan yada labarai Lai Mohammed

Alhaji Lai Mohammed

Ministan kula da al’adun gargajiya da kuma yada labarai, wasu na yi masa lakabi da “mai kwaskwarima” ganin yadda ya ke tallatawa da kuma kare manufofin gwamnatin Buhari da ha maza! Ha mata! Daga soke-soken da ta ke sha daga hannu ‘yan adawa da kuma ‘yan kasa, musammam a matsin da ake ciki na tattalin arziki.

Tanko Yakasai

Tsohon dan Siyasa kuma dan gani kashenin PDP da gwamnatin Jonathan, Alhaji Tanko Yakasai ya yi kaurin suna a Najeria a fuicinsa musamman a Arewacin kasar. A duk lokacin da ya bude baki ya yi magana sai Najeriya ta dauki dumi musamman arewacin kasar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel