Hotunan ma’aurata na ban dariya
1 - tsawon mintuna
Wasu hotunan ma’aurata sun watso a kafafen sadarwa daban daban na yanar gizo saboda irin tsarin da sukayi na daukan hotunan aurensu.
Hotunan wasu ma’aurata da ba’a bayyana sunayensu ba sun zamo abin ban dariya ga mutane, saboda ita amaryar tayi shiga ne irin na jami’ar hukumar kare haddura ta kasa, yayin da shi kuma mijin ya fito a matsayin direban da ya karya dokan tuki.
Hotunan sun cigaba da nuna Amaryar ta tare mijin nata, tana mai tambayoyi, sai dai daga karshen hotunan, sai aka ga direban ya fara soyayya da jami’ar hukumar kare haddura ta kasa, inda har ma ya amshi lambar wayarta.
KU KARANTA:Tsoffin ma’aurata masu sanya tufafi iri daya kullum
Asali: Legit.ng