Yarinya ta gane saurayinta ta gane saurayinta dan ludu ne
Wani mutum dan ludu wanda ya kwashe shekaru biyu yana soyayya da wata yarinya asirinsa ya tonu a tweeta.
Yarinyar mai amfani da @muvvabee a tweeta tace ta kadu sosai, bayan datayi kokarin shirya wani abun jinjina ga saurayin nata sakamakon kwashe shekaru 2 da sukayi suna soyayya.
Da abun ya bayyana, saurayin nata mai amfani da @eatdabootylikeg a tweeta ya dade yana yaudararta alokaci mai tsawo. Sannan kuma shi yafi kusanci da harkar ludu ( kuma yana ganin maza suna binta).
Asirin sa ya tonu ne sakamakon Yaron da yake harkar ludun nasa wanda yake amfani da @floprat da suke harkar a boye, ya nemeta domin ya gaya mata abubuwan dake faruwa tsakanin shi da saurayin nata. Gadai kadan daga cikin hirar nasu a tweeter:
Shekarun mu biyu da wannan saurayin nawa muna soyayya, gaskiya banji dadi ba. @muvvabee, yarinya ina da abunda zan gaya miki akan saurayin ki.
@floprat, duk abunda zaka ce kace anan ina jinka, Meye ya faru?
Sai saurayin yacema yarinyar, Wai ta dakatar da magana dashi da rufe shi gaba daya daga yin magana dashi, domin wannan mutumin dan ludu ne.
Haka dai hirar tasu ta kasance har asirinsa ya tonu. Inda saurayin daga baya ya yarda cewar shi dan ludu ne.
Allah ya kyauta.
Asali: Legit.ng