Wata 'yar bautar kasa musulma ta rasu

Wata 'yar bautar kasa musulma ta rasu

Wata 'yar bautar kasa ta rasu sakamakon wani mummunar hatsarin mota akan babbar hanyar Abuja ana sauran kwana daya ta gama bautar kasar nata kuma wata 2 kachal ya rage tayi aure.

Wata 'yar bautar kasa musulma ta rasu

Wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Muhammad Isa, ya sanya wannan mummunar labarin a shafinsa na Facebook game da aukuwar lamarin daya faru da 'yar dan uwan nashi, wacce ta rasu jiya 14 ga watan Satumba.

Abun tausayi ne kwarai da gaske wanda ya kamata ayima dangin ta jaje dangane da wannan babban rashin da sukayi.

Ya kara dacewa, " Wannan kyakkawar matar mai suna Hafsat Isah, wacce 'yar bautar kasace ta rasu akan babban hanyar Kaduna zuwa Abuja sakamakon mummunar hatsarin mota".

Yace: " Yace banyi tunanin zan tashi naji mummunar mutawar nata ba, sai gashi kwatsam na samu mummunar labarin mutuwar nata sakamakon hatsarin mota akan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Daman zata gama bautar kasar natane yau sannan kuma zatayi aure a watan Disamba nan mai zuwa. Amman Allah (SWA) yanada manufa a kanta"

"Allah ya amshi kyawawar aikin ki yarinyata Hafsat Isah"

Muna mika ta'aziyar mu ga 'yan uwanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel