Wasika: Shugaba Buhari, ka niya malamanmu albashinsu

Wasika: Shugaba Buhari, ka niya malamanmu albashinsu

Wani dalibin jami’ar Olabisi Onabanjo dake Ago-Iwoye jihar Ogun mai suna Ayodeji Oluwapelumi ya rubuta budaddiyar wasika zuwa ga Gwamna Ibikunle Amosun na ya biya albashin malaman jami’ar.

Ina rokon gwamnatin jihar Ogun tare da shugaban kasa Muhammadu Buhari dasu taimaka su biya malaman mu albasussukan du suke bi na watanni 24 don kawo karshen yajin aikin da malaman suka shiga. Za’a iya tunawa kungiyar malaman jami’ar OOU ta shiga yajin aikin dindindin saboda halin ko in kula da tace gwamnatin jihar na yi mata, na rashin biyan albashin sun a watanni 24.

KU KARANTA: Sakatariyar Ogun ta mutu sa’o’i 24 bayan an rantsar da ita

Kungiyar ASUU reshen OOU ta fara yajin aikin ne tun 8 ga watan agusta, inda tace “bai biya, ba aiki,” sakamakon haka an dakatar da jarabawar da daliban jami’ar suke rubutawa, sanadiyyar haka daliban ajin karshen ba zasu samu damar kammala karatunsu ba tare da sa’o’insu na sauran makarantun kasar.

Karin takaici ma shi ne yadda aka mana korar kare daga azuzuwan yayin da muke zana jarabawar mu bayan mun biya makudan kudaden makaranta da suka kai N104,000-N160,000, wanda shi ne kudi mafi tsada a jami’un kasar nan.

Bugu da kari, kowa ya riga ya san cewa gwamnatin jihar Ogun taki kashe ma makarantar kudi, babu kudin aikace aikace, dakuna bincike sun lalace, babu kayayyakin da zasu taimaki daliban kimiyya su fahimci karatu. A gaskiya harkar ilimi a jihar Ogun na cikin mummunar yanayi, don haka yana bukatan sauyi na gari.

Daga karshe ina kira ga duk masu kaunar ilimi, da masu kishin kasa dasu shigo cikin harakar nan, sa’annan su taimaka wajen rokan gwamna daya saurari kokekoken malaman mu, don kawo karshen yajin aikin.

Wannan ra’ayin da aka bayyana a cikin wasikar nan, ra’ayin marubucin ne, ba ra’ayin Legit.ng bane. Muna maraba da ra’ayoyinku, ku aiko mana ta infor@naij.com ko ka aiko mana sakon kart a kwana kana bin da kake son rubutu a kansa da dalilin da yasa kake son yin rubutun.

Za’a iya samun karin bayani na yadda ake aiko mana da labarai a shafin mu yanay gizo Legit.ng. zamu siya labarin ka: ka aiko mana labarai da hotuna. Sa’annan zaka iya neman mu don korafi, shawara ko yabo, kuma za’a iya samun mu a Facebok da Twitter.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng