An kama Jarumin Nolly wood
- Ifenyi Azodo sanannen jarumin Nollywood ne -
- An kamashi a Onitsha saboda zargin fashi
Yan sanda sun kama sanannen jarumin Nollywood Mr. Ifeanyi Azodo a Onitsha kan zargin yin fashi, komandar shiyar Abubakar Yahaya ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.
Yace" Akwai kara akanshi, dan Haka muka gayyace shi dan yin tambayoyi bayan haka muka bada belin shi, saboda laifin da yayi akwai damar yin beli, in kuma kuna son cikakken bayanin abinda ya faru, sai kuje gurin kakakin yan sanda na shiyar.
Ku fahimce ni, nace muna da kara da aka kawo a kanshi, muka gayya ce shi dan tambayoyi, yayin haka muka gano ya dauki hukunci da hannun shi kuma yayin bincike muka same shi da laifi dumu-dumu.
Haka kuma, mun samu kusan kashi 80 na abubuwan da aka rasa dan gane da lamarin, har yanzu dai muna kan bin cike, abinda muka samu a binciken shi ze dora mu ga abinda zamuyi cigaba.
Rohoton yace" Ifenyi ya gayyaci wani mutum dan shekara 30 wanda ake kira Stephen a wata hotel inda ya yada Zango a Onitsha, yayin da suke tattaunawa sun samu sabani wanda har ya ja hankalin ma'aikatan hotel din daga baya aka kira yan sanda.
PPRO, Asp Nkiru Nwode ya tabbatar da kama Ifenyi da akayi yace" Eh Lallai akwai karar da aka kawo kan fashi akan shi, ni ban ganshi a matsayin luwadi/ homo ba, sai dai kara da aka kawo akan fashi.
Asali: Legit.ng