Jonathan ya ziyarci Abdulsalam da Babangida a Mina

Jonathan ya ziyarci Abdulsalam da Babangida a Mina

Tsohon shugaban kasa Jonathan ya isa garin Mina na jihar Neja a ranar Talatar data gabata 13 ga watan satumba don kai ziyarar ban girma ga tsoffin shugaban kasa na mulkin soja.

Jonathan ya ziyarci Abdulsalam da Babangida a Mina
Jonathan da Babangida

Jonathan ya samu rakiyar tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnati Cif Mike Oghiadomhe ya gana da tsohon shugaban kasa janar Ibrahim Badamasi Babangida da tsohon shugaban kasa janar Abdulsalam Abubakar.

Sai dai ba’a samu cikakken bayanin ganawar ta tsoffin shuwagabannin kasar ba har zuwa yanzu, amma ana zaton ziyarar na gaisuwar Sallah ce kawai daya gudana a ranar litinin 12 ga watan satumbar 2016.

Shugaba Jonathan ya sanar da ziyarar ta shafinsa na Facebook inda yace “na kai ma magabata na kuma yayuna ziyara, janar Ibrahim Badamasi Babangida da janar Abdulsalam Abubakar, sa’annan zan zage karfina wajen karfafa dankon yan’uwantaka a tsakanin yan Najeriya”

Jonathan ya ziyarci Abdulsalam da Babangida a Mina
Jonathan da Abdulsalam

Sai dai shima Abdusalam a yayin da yake jawabi a babban masallacin garin Mina bayan an gabatar da sallar Idi, ya bukaci yan Najeriya da su daina lalata kayayyakin gwamnati.

KU KARANTA:Tsohon shugaban kasa Jonathan ya dawo gida Najeriya

Abubakar ya fadi haka ne a daidai lokacin da tsagerun Neja Delta ke cigaba da farfasa bututun mai a yankin don neman biyan bukatun su, da haka ne Abubukar yace kamata yayi tsagerun su mika korafinsu da bukatunsu ga hukumomin gwamnati ta hanyar data dace, yace daukan hukunci a hannunsu ba zai kawo cigaba ba a yankin, kamar yadda jaridar Daily Post ta ruwaito.

Jonathan ya ziyarci Abdulsalam da Babangida a Mina

Yace wanda wanann fashe fashen da lalata kayayyakin gwamnati da ake yi a wasu yankunan kasar nan ka iya kawo ci baya ga kasar nan, idan ba’a daina ba. Idan dai har zamu cigaba, dole ne mu daina lalata kayayyakin amfanin mu.” Daga nan sai ya bukaci yan Najeriya dasu baiwa shugaba Buhari goyon baya don ya samu damar shayar da kasar nan romon dimokradiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: