Ambaliyar Kogin jini a Bengladesh
Kwanaki kadan da wani kogin jini a kasar Rasha ya ta da hankalin jama’a, sai ga shi wani kogin jini ya mamaye Dhaka babban birnin Bengladeshi
A cewar rahoton jaridar The Sun, manyan titunan Dhaka sun cika da ruwan da launinsa ya koma ja zur! Wanda kuma daga baya aka tabbatar da cewa jini ne na gaske.
A cewar rahotanni, jinin da ya mayar da kogin ja, daga dubban dabbobin da ka aka yanka ne a bikin Sallar Layya a kasar a ‘yan kwanakin nan, an kuma kiyasta cewa na yanka dabbobi kimanin 100,000. In ji jaridar.
An kiyasta kasar Bengladesh na da kimanin Musulmai miliyan 148 da 600,000 a shekara ta 2011, kuma a bikin na sallar Layya da ake gudanarwa sau daya a shekara ana yanka dabbobin da suka hada da Raguna da tumakai da sauransu a kasar.
Sai dai wannan shekarar an gabatar da Sallar Layya ne a tsakiyar damina, a inda ranar Talata 13 ga watan Satumba ruwan sama ya yi ambaliyar ya mamaye lungu da sako na kasar, a inda magundanan ruwa masu jini, suka cukudu ruwan sama na ambaliyar, ya kuma kwarara zuwa titi.
Jaridar ta rawaito wata mace mai suna Attish Saha, wacce ta ke zaune a Dhaka na fadawa jaridar Guardian ta Burtaniya cewa, ganin wannan al’amari ya tayar mata da hankali matuka, domin a ruyuwarta ba ta taba ganin irin wannan al’amari ba.
Asali: Legit.ng