Tofa! Masana sun kirkiro wata bishiya mai bayar da

Tofa! Masana sun kirkiro wata bishiya mai bayar da

Daga kasar Manchaster na kasar Ingila, wani mai bincike ya kirkiro wata itaciya ta hanyar hada kwayar halittan dabba da na itaciya wanda a cikin shi danyen nama ne.

Wani bature Dakta Vincent Tarley wanda Darekta ne na kungiyar masana kimiyya shi ya kirkira, inda 'ya'yan itaciyar ke kama da lemu ko tumatir amma idan aka fere ciki danyen nama ne.

A cewarsa, "itaciyarmu na da matukar ban mamaki idan ka ji amma ba abun mamaki ba ne domin yana da sauki a duniya.

Tofa! Masana sun kirkiro wata bishiya mai bayar da
Tofa! Masana sun kirkiro wata bishiya mai bayar da

Masu rayuwa da ganye sun dade suna korafe-korafe dangane da kyamar nama da suke yi amma yanzun, suna iya cin 'ya'yan itaciyarmu. In ji Dakta Vincent

Ya ci gaba da cewa, "duk da dai ya dauke ni shekaru 12 kafin na kirkiri wannan itaciya amma sirrin yana da sauki."

Ya ce, sun dauki kwayar hallitar shanu sannan suka hada da kwayar halitta na itaciya, a lokacin da irin ya girma cikin itaciyar, maimakon ya haifo da 'ya'yan ittatuwa yadda aka sani, sai ya haifo da 'ya'yan ittaciya amma ciki idan ka tsaga yana dauke da danyen nama mai dauke da dandanon nama, har ma da karnin ko warin da nama ya ke da.

Wadanda suka ga safurin wannan 'ya'yan ittaciyar sun dandana naman kuma sun sheida da dandanon kamar na asalin nama ne.

Na yi matukar mamaki a karo na farko dana ci wannan dan 'itacen da aka gayamin bayan sun ya girma ne a jikin itace. Inji wani dan kasan Landan mai suna Mark Baker, Mai shekaru 41, wanda yana daga cikin wadanda suka halarci shirin "Consumer test" .

Ya ci gaba da cewa, sai dai yana da dandano ga dadi kuma babu wani ko irin ganye ganye a cikin shi ko kadan.

Naman da ya ke girma a jikin itaciya yana bukatar rana, ruwa da taki sannan yana da sauki da araha akan kiwon dabba. A cewar Dakta Tarley.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng