Ministan Abuja zai kori Almajirai da mabarata daga Abuja
- Ministan babban birnin tarayya Abuja ya umurci a kama duk mabaracin da aka gani a cikin birnin Abuja
- Ministan ya bada umurnin ayi wani shirin da zai tabbatar da cewan an mayar da su jihohin su
Shugabancin babban birnin tarayya Abuja suna shirya fidda wani tsari na kama mabarata da yan yawon bagaja a cikin birnin tarayya.

Ministan FCT ,Muhammadu Bello ya bayyana hakan ne a ziyarar da ya kai cibiyar sauya mutane da koyon aikin hannu watau Vocational and Rehabilitation Centre da ke Kuchiko ,Karamar hukumar Bwari a Abuja, yace za’a damke duka mabarata kuma a kawo su cibiyar.
Bello yace, za’ayi wani shirin yanar gizo ga FCTA wanda zai basu ikon samun sunaye da wasu abubuwa masu muhmmancin mabaratan domin mayar da su jihohin su.
KU KARANTA:Buhari zai fitar da Najeriya daga kangi da take ciki-Masari
Ministan kuma ya bada umurnin cewa sakatariyan cigaban jama’a na FCT su tabbatar da cewa an sanya sunayen wandanda aka kama a cikin shirin yanar gizo domin samun su. Kana, hukumar kula da yanayin cikin birnin Abuja watau Abuja Environmental Protection Board (AEPB) da kuma FCT Task Team on Environment sai sun daukin sunayen duka mabaratan kafin a kai su cibiyar inda jami’an social development zasu amshe su kuma kuma su mika su ga cibiyar.
Bello kuma ya bada umurnin cewa cibiyar ta fara shirin mayar da su jihohinda suka zo bisa ga dokokin ko wani Jiha inda kowani jiha zasu karbi jama’ansu
Shugaban cibiyar, Bala Tsoho ya fada ma ministan cewa ba da dadewa aka kawo mabarata da nakassasu 145 cibiyar ba. Yace kiwon lafiya da koshin lafiya mabarata da nakassasun ya inganta daga zuwan ministan.
Amma, yan najeriya da dama sun roki shugaba buhari cewa yayi murabus saboda mawuyacin halin da yan najeriya ke ciki a gwamnatinsa.
Asali: Legit.ng