Buhari zai fitar da Najeriya daga kangi da take ciki-Masari
Gwamnan jihar Katsina Aminu Bello Masari ya bukaci yan Najeriya dasu dage dayi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari addu’a don fitar da kasar daga tarin matsalolin da suka dabaibayeta.
Masari ya bayyana hakan ne bayan an gudanar da sallar Idi a Katsina ta hannun mai bashi shawara kan kafafen watsa labarai Abdu Labaran Malumfashi, sanarwar tace duk matsalolin da suke damun kasar nan babu wadda tafi karfin ayi maganinta. Masari ya kara da cewa ba shi da shakku kan shugaba Buhari wajen magance matsalolin kasar.
Masari yace “shugaban kasa Muhammadu Buhari ba sabon yanka bane a kan mulki, kuma matsalolin ba sabbi bane a wajen sa. Haka ma yah au mulki a shekarar 1983 kuma ya ceto kasar mu. Shugaban nada kishin kasa, zamu iya gane haka daga kamun ludayinsa ta yadda ya fuskanci matsalar tsaro.
KU KARANTA:Masari Ya Soma Binciken Magabanci Shi
“Allah ya kara mai do shi ne a wannan karon don ya kara maimaita kokarin da yayi a shekarun baya lokacin da tattalin arzikin kasar nan ya tabarbare. Kuma ina da yakinin zai cigaba da kokari idan mun bashi goyon bayan da yake bukata. Kazalika yana bukatar addu’ar mu.
A wani labarin kuma, shugaban kasa Muhammadu ya isa garin Daura a jihar Katsina ranar juma’a 9 ga watan satumba don gudanar da bikin babbar Sallah. An hange shi tare da Masari a filin jirgin jihar.
Sa’nnan shugaban ya gana da Alh Sa’idu Barda, tsohon gwmanan Katsina, Alh Mannir Yakubu, mataimakin gwamnan Katsina, Sarkin Katsina Abdulmuminu Kabir Usman da sauran manyan mutane.
Asali: Legit.ng