Dan Najeriya mai safarar kwayoyi ya shiga hannu

Dan Najeriya mai safarar kwayoyi ya shiga hannu

Hukumar yaki da shan miyagun kwayoyi (NDLEA) ta kama shahararren mutumin nan Abiodun Israel Banjo daya kware wajen safarar kwayoyi bayan ta kama shi da daurin hodar ibilis.

Dan Najeriya mai safarar kwayoyi ya shiga hannu
Abiodun Banjo

Kafar watsa labarai ta Sahara Reporters ta ruwaito an cafke Banjo dake zaune a garin Pretoria na kasar Afirka ta kudu ne a filin tashin jirgin kasa da kasa na Murtala Muhammad dake jihar Legas sakamakon ganin sa da aka yi dauke da haramtattun kwayoyi.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar NDLEA, Mitchell Ofoyeju ya bayyana cewa an kama Banjo ne a daidai lokacin da ake tantance matafiya masu shirin tafiya kasar Afirka ta kudu. An kiyasta jimillar darajar kwayoyin kan naira miliyan 31.

Shugaban hukumar NDLEA reshen filin tashin jiragen, Ahmadu Garba ya bayyana cewa binciken jakukkunan matafiya da aka yi ne ya tabbatar da akwai daurin ledoji biyu na hodar ibilis da aka nade su da kayan sawa cikin jakan Banjo. Sai dai Banjo, wanda ake zargin, yace ba shi da masaniyar kwayar a cikin jakansa, asali ma an bashi sako ne ya mika ma wani.

“ina aiki a Pretoria ne, abokina da muke tare da can kasar Afirka ta kudu ne ya roke ni da in amsan mai kayayyakin abinci daga wajen kaninsa, inda ma yayi alkawarin biyana dala dubu biyu. A gaskiya sai da na binciki kayan da kyau, amma ban ga wani mugun abu a ciki ba, daga nan ne na yarda in dauki jakukkunan. “don haka ne nayi mamaki matuka da aka tsinci wadannan kwayoyi a cikin jakkunan. Nayi bakin ciki ganin cewa abokina ne ya shirya min wannan.”

KU KARANTA:NDLEA ta cafke masu safara 184, da kwace 96kg na miyagun kwayoyi

Shugaban hukumar NDLEA na kasa Muhammad Mustapha Abdullahi ya gargadi jama’a da su kula da irin dabarun kwararrun masu safarar miyagun kwayoyi.

Dan Najeriya mai safarar kwayoyi ya shiga hannu
hodar iblis din a daure cikin kaya da abinci

“Masu safarar kwayoyi su kan dauki hayar yan zauna gari banza, sa’annan sun kware wajen iya boye kwayoyin, domin mun sha kama kwayoyi a cikin kayan abinci, na’urori, kayan sawa da makaman tansu. Don haka muna gargadin matafiya dasu dinga daukan jakukkunan su da kansu, kuam su guji daukan jakar dab a nasu ba.” Daga karshe ya kara da cewa jahilci ba uzuri bane.

Ga abin da dokar yaki da fataucin kwayoyi tace “doka zata kama mutum da laifin safarar kwaya idan ya dauko, ya kawo ko ya ajiye kwaya a duk tashar hukumar shige da fice kamar su filin tashin jirgi, tashar jirgin ruwa, da makamantansu.”

Asali: Legit.ng

Online view pixel