Muhimman labarun ranan talata
Jaridar Legit.ng ta tattaro mana muhimman labarun da sukayi kanin labarai a ranan Talata, 13 ga watan Satumba.
1.Yan bindigan Neja Delta sun sake kai hari, sunyi barazana cigaba da kai wa
Wasu yan bindigan neja delta sun kai hari wani kafan mann NPDC da ke Afiesere-Iwhrenene a jihar delta. Kungiyar The Niger Delta Greenland Justice Mandate ne suka dau alhakin kai harin da aka kai misalign karfe 1 na dare a rana litinin.
2.Father Mbaka yay a sake fadin wata Magana akan gwamnatin shugaba Buhari
Mbaka yace Buhari na aiki da wadanda suke son ganin karshen shi
Shugaban Adoration Ministry, Rev Fr Ejike Mbaka, yace shugaba muhammadu buhari yana aiki da wasu mutane wadanda basu son ganin ya ci nasara.
3.Dalilin da yasa zan ki aiki a gwamnatin buhari idan aka nemeni inyi - Okonjo-Iweala
Tsohuwar ministan kudi, Okonjo-Iweala tace baza tayi aiki a gwamnatin buhari ba ko da shugaba buhari ya neme ta da tayi aiki a gwamnatinsa.
4.Goodluck Jonathan ya kaima Babangida da Abdulslam ziyara
Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kaima tsaffin shugabannin kasa 2 ziyara a jihar Neja a ranan talata ,13 ga watan Satumba.
5.Wani yayi mumunan martani ga yarinyar Buhari
Kwanakin baya ne ‘yar autar shugaban kasa,Muhammadu Buhari ,Zahra, ta ke tambayen yan najeriya matsalolinsu ta shafin sad zumunta ta twita la’alla zata iya taimaka musu ,amma wani yayi mata mumunan martani.
6.Sojin ka na tsoron mutuwa,sai nutse wa suke cikin ruwa – Avengers ga Buhari
Yan kungiyan Niger Delta Avengers (NDA), suna dariya ga shugaban kasa muhammadu buhari cewa sojin shin a ta mutuwa a horon “Crocodile Smile.”
7.Rundunar Sojin Najeriya sun kwace rafukan Neja Delta
Rundunar sojin najeriya sun saki bidiyo da ke nuna yadda rundunar ke horo a ‘operation crocodile smile’. Jaridar vanguard ta bada rahoto.
8.Ezekwesili ta musanta kushe Shugaba Buhari akan tattalin arziki
Tsohuwar ministan Ilimi, Oby Ezekwesili, ta musanta rahotannin da ke cewa ta daura laifin durkushewar tattalin arzikin kasa kan shugaba Muhammadu Buhari.
9.‘ku manta da Biafra, nayi yaki ne domin hadin kan Najeriya
Shugaban kasa Muhammau Buhari yayi kira ga matasan najeriya da suyi iyakan kokarinsu domin dawo da karfin najeriya ta hanyar neman ilimi,kishin kasa da kuma abubuwan da zasu kawo hadin kai.
Asali: Legit.ng