Ka shiga taitayinka: PDP sun gargadi Falana

Ka shiga taitayinka: PDP sun gargadi Falana

Jam’iyyar PDP reshen jihar Ekiti ta gargadi fitaccen lauya Femi Falana da hawainiyarsa ta kiyaye ramar gwamna Fayose, ya daina yin batanci ga gwamnan, inda suka shawarce shi da yaje can yaji da burinsa na zama gwamnan jihar Ekiti.

Ka shiga taitayinka: PDP sun gargadi Falana
Femi Falana

Jam’iyyar PDP tace duk irin batancin da Falana tare da ire irensa zasu yi ma gwamna Fayose, hakan ba zai taba rage darajar gwamnan ba a jihar Ekiti da kasa baki daya.

PDP ta fitar da wannan bayani ne a matsayin martani ga Femi Falana biyo bayan zargin da yayi na cewa gwamna Fayose na satan kudaden jihar a wani taro a Legas. Sanarwar ta samu sa hannun sakataren watsa labarai na jam’iyyar PDP a jihar Ekiti Mista Jackson Adebayo inda yace ta tabbata Falana yayi nisa wajen nuna kiyayya ga gwamna Fayose.

PDP tace “duk da cewa ya kamata ace munyi watsi da zancen Falana kamar yadda muka saba sakamakon mun fahimci tsananin munafuncinsa, amma abin kunya ne ace babban lauya kamar Falana zai dinga kiran wani barawo, alhalin ba wata kotu da ta tabbatar da haka”

PDP ta kara da zargin Falana da cewa yana amfani da alakarsa da hukumar EFCC wajen yin batanci ga gwamna Fayose, tace “ya kamata Falana da ire irensa su fahimci bambamci tsakanin 2006 da 2016. Basu isa su mayar da jihar Ekiti baya ba, kamar yadda sukayi a shekarar 2006.”

KU KARANTA:Gwamnonin PDP sun maganta akan Ali Modu Sheriff

Daga nan sai Jam’iyyar ta baiwa Falana shawarar yaje ya cika gaba da kokarin cika burinsa na zaman gwamna, ya daina tallata kiyayyarsa ga Fayose.

Fayose ya kada Falana a sheakarar 2003, sa’annan ya kara kada Falana tare da hadakar tsoffin gwamnonin jihar su uku a 2014. Don haka sai yafi dacewa ga Falana ya fuskanci zaben 2018, ba wai ya dinga yayata karairayi ba akan gwamana Fayose, domin hakan ba zai shi zama gwamnan Ekiti ba.

A maimakon ya dinga boyewa da sunan mai karajin kare hakkin dan adam yana hura wutar rikici a jihar Ekiti, kamata yayi Falana ya fito a mutum ya bayyana sha’warsa na zaman gwamna, wanda dama abu ne a bayyane, daga nan sai muka gudun ruwarsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng