Fulani makiyaya da hare-haren Enugu

Fulani makiyaya da hare-haren Enugu

Sarkin Hausawan Enugu ya bayyana dalilin da ya sa Fulanai Makiyaya ke yawan kai hari a kauyukan da ke jihar a dai dai lokacin da jama’ara jihar Ebonyi ke bore kan mamayar Fulanin

Fulani makiyaya da hare-haren Enugu

Shugaban al’ummar Hausawa a Enugu, Abubakar Sambo ya bayyana dalilin da ya sa ake samun yawaitar hare–haren Fulani Makiyaya a jihar Enugu da cewa nan ce babbar hanyar makiyayan da shanunsu zuwa yankin kudu.

A cewar jaridar Vanguard, shugaban ya yi wannan furuci ne a hirarsa da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya NAN ne, a inda ya kuma ce, kashi 90 na makiyayan da suka fito daga arewacin kasar zuwa yankunan kudu maso gabas, da kudu maso kudu, kan bi ta babbar hanyar mai cinkoso ta kwanar mil 9 da ke Ngwo a Enugu don zuwa inda za su je a kudu.

Abubakar ya kuma kara da cewa, “…dole ne sai ka bi ta Enugu kafin ka je yankin kudu maso kudu, ko kudu maso gabas, domin wasun su na bi ta cikin jihar Kogi zuwa karamar hukumar Uzo Uwani a jihar Enugu, ta wannan hanyar ce wadanda suka kai hari a Nimbo suka bi’.

Basaraken ya kuma kara da cewa, yawancin makiyayan, Fulanin tashi ne da suka yanke shawarar yin kaka-gida a wasu kauyukan jihar a kan hanyarsu, wannan a cewar shugaban Hausawan, shi ya sa ba a rabo da hare-hare a jihar ta Enugu.

A ‘yan kwanakin nan ne wani bafullatani ya koka da cewa an kai hari kan garken shanunsa a inda dansa ya bace tare kimanin shanun 100 a jihar Enugu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng