An kama faston katolika da yima reverend sister ciki
Coci ta sanya takunkumi ga wani faston katolika da yayi ma wata mai riko da addini ciki.
Bisa ga labarin da aka samu ya kasance yana kwana da ita kuma ta samu juna biyu yanzu, wanda yayi mata ciki shine Father Kevin Mthunzi Takaendesa na cocin Bulawayo, Zimbabwe.
Yayinda ake magana kan al'amarin, shugaban cocin,Father Alex Thomas , ya kori faston da sistan daga cocin ,yace:
“An hukunta father kelvin saboda yi ma mai riko da addini ciki kuma na rubuta. Amma ya tafi kasar ingila wanda dama ya shirya yi tun farkon shekara, kuma kun san yadda zuwa ingika ke da tsada. Akwai dokokin mu a ko ina mai suna Code of Canon Law wanda ake hukunta duk mamban da yayi laifi da shi.”
KU KARANTA:Oshiomole yace an kori Osagie Ize-Iyamu yayinda yake Jami’ar Benin
Ina tabbatar muku da cewa father takaenesa ya tafi ingila kuma ya dawo coci. Hutun da ya dauka bata da alaka da cikin da ya ma mace. Na san ana maganganu da dama a kaina da wasu fastoci . Amma ni dai ban tura kowani fasto ingila ba bayan yayi ma mace ciki kuma ban koreta daga cocin ba.
Asali: Legit.ng