Wata mace mai gemu
1 - tsawon mintuna
Baiwar gemu mai tsawon inci shida da Allah ya horewa Harnaam Kaur, da ke Slough, Berkshire, na kasar Burtaniya, ya sa ta yi nasarar shiga kundin tarihin duniya (Guinness Book) a matsayin mace kuma matashiya mai shekaru 24 da ta mallaki gemu.



Matashiyar wacce 'yar asalin kasar Indiya ce ta yi farin ciki da daukakar da ta samu a dalilin baiwar gemun da take da shi domin ya sa ta samu daukaka a duniya.
Asali: Legit.ng