Nigeria ta cira tuta a gasar nakasassu ta Duniya

Nigeria ta cira tuta a gasar nakasassu ta Duniya

Wata mai wasan daga nauyi da ta waklici Najeriya a gasar wasannin motsa jiki na nakasassu ta ci wa kasar lambar Tagulla

‘Yar wasan daga nauyi mai suna Latifat Tijjani ta ci wa Najeriya Lambar Tagulla a gasar wasannin motsa jiki na nakasassu mai suna Paralympic, da ake gudanarwa a yanzu a birnin Rio ta kasar Brazil.

Nigeria ta cira tuta a gasar nakasassu ta Duniya
Latifat Tijjani a kujerar guragu, ta zo ta biyu a gasar daga nauyi ta duniya na Paralympic

Tijjani wacce ta shiga gasar mata masu daga nauyin kilogiram 45, ta zo ta biyu ce a lokacin da ta daga karfe mai nauyi kilogiram 106, watau kilogiram daya kacal a bayan Hu Dandan wata ‘yar kasar China da ta daga karfe mai nauyin kilogiram 170, ta kuma kafa tarihi.

A baya dai Nigeria ta lashe dukkan lambobin Zinaren 6 na irin wannan gasar da aka yi birnin Landan ta kasar Biritaniya a shekara ta 2012.

Za a iya cewa Nigeria ta fita da kafar dama da wannan nasara da fara samu na lambar Tagulla, kuma Latifat ta sa dan ba ga sauran ‘yan wasan daga kasar da ke goyyaya da takwarorinsu na duniya a gasar wasannin na Paralympics da ke yi a Rio a halin yanzu.

A kowanne lokacin bayan gasar guje-guje da tsalle-tsalle na Olympics a kan yi irinsa na nakasassu zalla bayan an kammala waccan, kuma Najeria ta tura ‘yan wasanta nakasassu zuwa Rio domin karawa da ‘yan uwansu na duniya a wasannin motsa jiki daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng