kalli adon gashi iri-iri da ake sanya atamfa dashi da yake mace
Mun gode Allah yau juma'a!
Ako yaushe akwai abunda mutum zaisa kuma ya godema Allah akan sa. Muna murna domin kuwa yau Juma'a, mun kusa shiga makon karshe, munsan yadda abubuwan suke idan mukayi shigar kananan kaya daga ranar Litinin zuwa ranar Alhamis, saboda haka ranar Juma'a itace ranar data kasance yawancin mutane suna sanya kayan su na al'adar su.
Ranar Juma'a shine farkon ranar da mutum yake dashi na gaisawa da 'yan uwa da abokanan arziki, sannan kuma zasu iya zuwa wasu wuraren da mutum yakeso yaje.
Kayan da aka sanya na atamfa, amfi sanyasu ne a ranar Juma'a wanda ake dinka su a yanayi iri-iri, wanda akan dunka su domin sawa a ranar Juma'a, dakuma wanda ake dinkawa domin ajen fati sai kuma wanda ake dinkawa domin zaman gida kokuma zuwa wani waje daban.
Kalli wadannan da suka sanya atamfar da akayi musu dinki kala-kala.
Asali: Legit.ng