Cututtukan da ruwa ke maganinsu
Ruwa shine yalwataccen sinadari mafi muhimmanci a rayuwa, a don haka yake da amfani daban daban.
A gaskiya kamata yayi ace ruwa shine mafi soyuwa cikin kayan shaye shaye, saboda a yayin da dan adam ka iya kwashe sati uku ba tare da cin abinci ba, ba zai iya kwashe kwana uku ba tare da shan ruwa ba.
Don haka zamu bayyana cututtuka biuar da ruwa ke magani.
Ciwon zuciya ya zama ruwan dare a tsakanin mutane, kuma a kullu yaumin yana kara gagarar magani. Amma a sani ruwa nada alaka da ciwukan da suka shafi zuciya. Bincike ya nuna shan kofi 5 na ruwa a rana na rage yiwuwar kamuwa da ciwon zicuya da kasha 50.
Ana iya maganin ciwon amosani idan mara lafiyar na yawan shan ruwa. Ruwan zai taimaka wajen kawar da sinadaran dake taruwa a jikin masu samar da amosanin (kamar su uric acid)
Shan ruwa yadda ya kamata zai taimaka wajen baiwa koda cikakken lafiya, ta hanyar wanke shi, saboda aikin koda da hanta ne fitar da duk wani nau’in datti a jikin dan adam.
KU KARANTA:An dauki dan shekara biyu zuwa Abuja dan neman magani
A dukkanin gabban dan adam akwai wasu abubuwa dake dauke da sinadari na musamman, amma idan ya kasance akwai karancin ruwa a cikinsu, sai jikkunan mu su janyo ruwa daga sinadaran, daga nan sai gabban mu su fara zafi sakamakon ruwa daya kare musu. Don haka shan ruwa na maganin amosanin gabbai.
Shin ko kasan shan kofi 2 na ruwa zai kara yawan hanzarin aiki a jikin ka da kasha 30? Bincike ya nuna cewa shan kofi 6 na ruwa a yini zai narka kitse na sama da kilo 2 a jikin dan adam a shekara.
Asali: Legit.ng