Hanyoyin faranta ma uwargida rai, a halin rashi

Hanyoyin faranta ma uwargida rai, a halin rashi

 Idan dama can kai mai yawan bindiga da kudi ne, kuma baka tari, toh tabbas a yanzu ka shiga halin babu sakamakon lalacewar tattalin arziki dake addabar Najeriya

Hanyoyin faranta ma uwargida rai, a halin rashi
Couple fighting

Don haka shin kana son ka dinga faranta ma matarka rai cikin wannan yanayi? Wannan abu ne mai sauki kam. Sai dai kash! Mazaje da dama basu san haka ba, sai kaga suna ta fama da iyalinsu a wannan marar.

Ka yawaita aika mata sakon kar ta kwana, matarka za tayi farinciki matuka ko dan yaya ka aika mata tes, Gajeren tes kamar ‘Ina tunaninki’ ya isa tun da dai ta san baka da isashshen kudin kiranta.

Ka kasance a duk dare kana gida don samun dauke mata kewa, ka sayo kasukan bidiyo kuyi ta kallo cikin farin ciki da annushuwa, hakan zai rage maka kashe kudin da zakayi da ace ka fita zuwa silma.

Irin wannan halin karyewar tattalin arziki na sanya namiji shiga taitayinsa dangane da kashe kudi, duk hidimar da ka san ba zaka daure yin taba, toh ka daina. Wasu mutane sun fi son su gudanar da kasaitaccen bikin a ranaku murnan haihuwa, aure, da sauransu. Shawara a nan shine, miji yayi bikinsa da matarsa kadai, hakan zai rage kudin da zasu kashe.

Ya kamata miji ya gane kowa na kokawa da radadin karyewar tattalin arzikin nan, don haka kada miji ya dinga huce haushinsa a kan matarsa tamkar itace ta janyo matsalar tattalin arzikin.

KU KARANTA:Wasu Iyali Sun Rasa Rayuwar Yayansu Guda 2

Ku dage da addu’a musamman a lokuttan Sallah ko kafin cin abinci, da sauran lokutta, har Allah ya kawo saukin abin.

Na kan rasa menene a ciki idan namiji yace matarsa ‘kiyi hakuri’, kai kace wani aikin gabas aka sanya su. kananan kalamu kamar wannan na sanyaya ma uwargida rai. Idan miji ya fada ma uwargida Kalmar nan, haka zai sanyata jin dadi, da samun tabbacin kauna daga gareshi.

Ya kamata ace iyali na samun nishadi lokaci zuwa lokaci ta hanyar bayar da labaran barkwanci, na tabbata akwai irin abubuwan ban dariya da ka taba yi, ka bata labarinsu, ita ma ta baka nata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng