Dalilin da yasa muka daga zaben jihar Edo- INEC

Dalilin da yasa muka daga zaben jihar Edo- INEC

Hukumar gudanar da zabe mai zaman kanta INEC ta yarda da shawaran daga zaben gwamnan jihar Edo da sati biyu saboda dalilai da suka shafi tsaron kasa.

An daga zaben da ya kamata a gudanar ranan asabar 10 ga watan satumba  ne a wata ganawar tsaro da akayi a Benin, babban birnin jihar. Jaridar punch ta bada rahoton.

Dalilin da yasa muka daga zaben jihar Edo- INEC
Edo election contenders

Hukumar ta fada ma manema labarai a wata hiran da ta gabatar misalin karfe 8.00 na yamma a Benin, cewa an daga zaben ta dalilin shawarwarin da jami'an tsaro suka bada.

Zaku tuna cewa Hukumar yan sandan najeriya, Hukumar masu lekan asiri,DSS, sun jawo hankalin INEC da ta daga zaben saboda tabbatar da tsaro.

KU KARANTA:Abubuwa 5 da ka iya faruwa a sakamakon dage zaben Edo

Yayinda hukumomin tsaron suka yi Magana a wata hira da yan jaridu a ranan 7 ga watan Satuma, kakakin jami’an yan sanda Dan Awunah yace wasu yan boko haram na shirin yin aika-aika a jihar a ranan zaben.

Awunah yace sun samu  rahoton ne kaffifin da suka amince da labarin su. Duk da cewan hukumar INEC ta ce zata babu gudu ,ba ja da baya, daga baya ta hakura ta daga zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng